logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya za ta matsawa ma’aikatanta karbar rigakafin COVID-19

2021-10-14 20:16:12 CRI

Gwamnatin Najeriya za ta matsawa ma’aikatanta karbar rigakafin COVID-19_fororder_1615357192205084111

Gwamnatin Najeriya ta ce daga ranar 1 ga watan Disambar karshen shekarar nan, sai ma’aikatan ta da suka nuna shaidar sun karbi rigakafin COVID-19 ne kadai za su samu izinin shiga ofisoshin gwamnati.

Da yake tabbatar da hakan, yayin wani taron manema labarai da aka gudanar jiya Laraba a birnin Abuja fadar mulkin kasar, sakataren gwamnatin Najeriyar Boss Mustapha, ya ce matakin wani yunkuri ne na karfafa gwiwar ‘yan Najeriya su amince da karbar rigakafin.  (Saminu)