logo

HAUSA

MDD tana maraba da sabunta yarjejeniyar zaman lafiyar Mali

2021-10-13 14:27:47 CRI

MDD tana maraba da sabunta yarjejeniyar zaman lafiyar Mali_fororder_1013-Mali-Ahmad

MDD tana maraba da sabunta yarjejeniyar zaman lafiyar kasar Mali wanda dukkan bangarorin kasar suka amince a aiwatar, da kuma tsarin da gwamnatin kasar ta gabatar na sauya tunanin tsoffin mayakan kasar.

Kakakin MDD ya bayyana a jiya Talata cewa, sun yi maraba da sabunta yarjejeniyar zaman lafiyar bisa amincewar bangarorin kasar bayan kammala taron kwamitin sanya ido wanda ya gudana a Bamako, kamar yadda Stephane Dujarric, kakakin babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana.

Dujarric ya bayyanawa taron manema labarai cewa, abokan aikinsu na MDD sun yi maraba da sanarwar da gwamnatin kasar Mali ta fitar game da kudirinta na sauya tunanin tsoffin mayaka 13,000 ya zuwa karshen wannan shekara, da kuma karin wasu mayakan 13,000 nan wasu shekaru biyu zuwa uku masu zuwa, a matsayin wani bangare na shirin aje makamai na kasa da kasa, da kuma shirin kawar da mayakan da gyaran halinsu a Mali.

Sannan yace, suna kuma maraba da aniyar da bangarorin kasar Mali suka nuna na amincewa da shirin kyautata rayuwa da tattalin arzikin tsoffin mayakan da suka riga suka yi rejista, wanda ya kumshi har da mata kusan 300 daga kowace shiyya. (Ahmad)