logo

HAUSA

Kamfanin Sin ya fara horas da matasan Zambiya don inganta kwarewarsu

2021-10-13 14:35:54 CRI

Kamfanin Sin ya fara horas da matasan Zambiya don inganta kwarewarsu_fororder_1013-Zambia-Ahmad

Wani kamfani mallakin kasar Sin ya fara aikin horar da matasan kasar Zambiya a fannonin sana’o’i daban daban da nufin inganta kwarewarsu, kamar yadda wani jami’i ya bayyana.

CAMCO Group, wani kwamfani ne dake samar da kayayyakin aikin gona, ya kafa wata cibiya da nufin samar da kwararrun injiniyoyi.

Li Tie, shugaban kamfanin, ya bayyana a wajen bikin yaye matasan da aka baiwa horon a fannin gyaran taraktocin noma a Lusaka, babban birnin kasar cewa, horon zai taimakawa matasan wajen samun kwarewa a fannoni daban daban na gyaran manyan motocin noma domin su samu damar dogaro da kansu a matsayin injiniyoyi.

Ministan kimiyya da fasaha na kasar, Felix Mutati, ya bayyana cewa, fannin noma na zamani a kasar yana fuskantar koma baya sakamakon karancin kwararrun da za su taimaka wajen kara bunkasuwar fannin.

Ministan na Zambia, wanda ya halarci bikin, ya yabawa kamfanin na kasar Sin bisa bullo da shirin bada horon wanda a cewarsa zai taimaka wajen kirkiro damammaki na samar da guraben aikin yi da sana’o’in dogaro da kai. (Ahmad)