logo

HAUSA

Sin ta bayar da shawarwari kan yadda za a gina rayuwar al'umma a doron kasa

2021-10-13 14:21:17 CRI

Sin ta bayar da shawarwari kan yadda za a gina rayuwar al'umma a doron kasa_fororder_1013-Rui-Ping-Ibrahim

Jiya ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron kolin shugabannin sassa na 15 kan mabambantan halittu tare da gabatar da muhimmin jawabi. Yayin jawabin nasa, shugaba Xi ya yi cikakken bayani kan wasu jerin manyan batutuwa, kamar wane irin gida ya kamata a gina, yadda za a gina shi, da yadda kasar Sin za ta yi, yana mai nuna alkiblar gina rayuwar al'umma a doron kasa. Yana mai cewa, kare halittu masu rai, yana taimakawa wajen kula da kasar dake duniyarmu da ma inganta dorewar ci gaban bil'adama.

Nau’in halittu shi ne ginshikin rayuwar dan adam da ci gabansa. Sai dai kuma, yanayin kasa a halin yanzu, yana kara shiga cikin hadari. Wani rahoton MDD mai alaka ya yi nuni da cewa, ana asarar halittu masu rai a cikin yanayin da ba a taba gani ba, kuma "lokaci yana kurewa." Ga dan adam, "wace irin al'umma ce ke rayuwa a doron kasa, ya kamata mu gina tare" ta yadda za ta zama tambayar gaggawa kuma dole ne a amsa.

A taron farko na duniya da MDD ta gudanar mai taken wayewar kan muhalli, duniya ta ji "amsar da kasar Sin ta bayar". Wato, gina gida a doron ƙasa wanda mutum da yanayi ke rayuwa cikin jituwa, tattalin arziki da muhalli suna bunkasa tare, kuma kasashe a duk faɗin duniya, su ma suna habaka tare. (Ibrahim Yaya)