Cinikin wajen da kasar Sin take yi na bunkasa yadda ya kamata
2021-10-13 20:50:35 CRI
Babbar hukumar kwastam ta kasar Sin, ta fitar da sabbin alkaluma a yau Laraba, wadanda suka bayyana cewa, daga watan Janairu zuwa Satumbar bana, jimillar kudin cinikin shige da ficen hajoji ta Sin ta kai kudin kasar Yuan triliyan 28.33, adadin da ya karu da kaso 22.7 bisa dari, in an kwatanta da makamancin lokacin bara. Alkaluman sun shaida cewa, yawan kudin hajojin da aka fitar ya karu da kaso 22.7 bisa dari, yayin da yawan kudin shigo da kayayyaki ya karu da kaso 22.6 bisa dari.
Ana iya ganin cewa, harkokin shige da ficen kayayyaki na kasar Sin na bunkasa cikin sauri, al’amarin da ya shaida cewa, kasuwancin wajen da kasar Sin take yi na bunkasa yadda ya kamata.
A matsayinta na babbar kasa ta farko dake gudanar da cinikin hajoji a duk duniya, farfadowar cinikin waje na kasar Sin na da matukar muhimmanci ga tabbatar da harkokin masana’antu, da samar da kayayyaki a duk duniya. Tun farkon bana, cinikin wajen da kasar Sin take yi yana kan gaba a duniya. Kuma a farkon rabin shekarar da muke ciki, yawan kudin harkokin shige da ficen ya dauki kaso 13.2 bisa dari na kasuwar duniya, kana yawan kudin fitar da kaya ya dauki kaso 14.5, yayin da yawan kudin shigo da kaya ya dauki kaso 12 bisa dari na kasuwar duniya.
Dukkan wadannan abubuwan sun shaida cewa, kasar Sin na kara bude kofar kasuwarta ga duk duniya, a wani kokari na more damammakin ci gaba tare da kamfanonin duniya. (Murtala Zhang)