logo

HAUSA

Jihar Bayelsa ta Nijeriya na neman jarin kasar Sin a bangaren aikin gona

2021-10-12 09:50:43 CRI

Jihar Bayelsa ta Nijeriya na neman jarin kasar Sin a bangaren aikin gona_fororder_1012-faiza-2-Bayelsa

Jihar Bayelsa dake kudancin Nijeriya, ta nemi kasar Sin ta zuba jari a bangaren aikin gona na jihar, domin taimaka mata raya shirinta a bangaren.

Wata sanarwa da aka fitar jiya, bayan taron da gwamnan jihar Douye Diri ya yi da Jakadan kasar Sin Cui Jianchun a karshen makon da ya wuce a birnin Abuja, ta ruwaito gwamnan na cewa, jihar ta riga ta gano bangaren aikin gona a matsayin mai muhimmancin da zai kai ga samar da ci gaba mai dorewa.

Gwamnan ya kara da cewa, sun riga sun gano bangarori 4 da za a iya zubawa jari da suka hada da kamun kifi da noman shinkafa da rogo da kuma plantain.

Har ila yau, ya ce kasar Sin ta samu gagarumar nasara a bangaren raya tattalin arziki da kawar da talauci, kuma ta yi alkawarin hada hannu da kasashe masu tasowa kamar Nijeriya wajen yakar talauci, karkashin dandamali irin na shawarar Ziri Daya da Hanya Daya. (Fa’iza Mustapha)