Sharhi:Mu hada kai don kare mabambantan halittu a fadin duniya
2021-10-12 21:52:56 CRI
Yau da watanni da suka gabata, “bulaguro” da wasu giwayen da suka yi ya jawo hankalin duniya kan lardin da na fito, wato Yunnan.
Lardin Yunnan yana kudu maso yammacin kasar Sin. A watan Afrilun wannan shekara, wasu giwaye nau’in Asiya sama da 10 sun bar muhallinsu na ainihi da ke yankin Xishuang Banna na lardin Yunnan sun doshi arewa, har sun isa yankin birnin Kunming, hedkwatar lardin Yunnan, wanda ke da kilomita sama da 500 daga Xishuang Banna din. Sai dai bayan da suka shafe sama da kwanaki 110 suna bulaguro na tsawon kilomita 1300, a watan Agustan bana, sun koma ainihin muhallinsu.
Kafofin yada labarai sama da 1500 da suka zo daga kasashe da yankuna fiye da 180 sun ba da labaran giwayen, wadanda suka yi matukar janyo hankalin al’ummar ketare. Giwayen sun burge wadannan baki da ke bibbiyarsu a kai a kai a kasa da kasa, wadanda kuma suka yaba da gwamnatin kasar Sin, da ma al’ummar kasar dangane da yadda suka yi kokarin ba da kariya ga giwayen.
Abin haka yake. Bayan da giwayen suka bar muhallansu, mazauna wuraren da giwayen suka ratsa, da mahukuntan lardin Yunnan, sun tura dimbin ma’aikata domin samar da kariya ga giwayen, da ma bin sawun giwayen tare da yi musu jagora, duk da tarwatsa mazauna wuraren da giwayen suka ratsa. Bayanai na cewa, ya zuwa ranar 8 ga watan Agusta, gaba daya an tura ‘yan sanda da sauran ma’aikata dubu 25, da kuma jiragen sama marasa matuki, don su shiga wannan aiki, baya ga haka, an kuma tarwatsa al’umma sama da dubu 150, tare da zuba abinci kimanin ton 180 ga giwayen. Ban da haka, mazauna da ma kamfanoni na sassan da giwayen suka ratsa, sun nuna hakuri sosai da giwaye. A birnin Yuxi, giwayen sun shiga gonaki na manoma, tare da cinye musu hatsin da suka shuka, amma manoma sun yi hakuri sosai, sun ce a bar su su ci, ba damuwa, za mu sake yin shuka a shekara mai zuwa. Sai kuma a yankin Honghe, mazauna wurin ba su gudanar da shagulgula ba a yayin bikinsu na gargajiya, don kada su tsorata da giwayen.
Bayan da giwayen suka kama hanyar komawa muhallansu na ainihi, masana’antun sassan da suka ratsa sun daina aiki tare kuma da kashe fitilu, don su wuce wurin ba tare da sun ji tsoro ba, lalle lamuran ba sa lisaftuwa, wadanda suka shaida yadda ‘yan Adam ke zaman jituwa da halittu, kuma ni a matsayin ‘yar garin, na yi alfari da abin da ya faru a garinmu.
Har yanzu ba a tabbatar da dalilin da ya sa giwayen suka yi “bulaguron” ba, sai dai wasu cikin raha na cewa, ta yiwu giwayen sun san cewa za a kira taron kasashen da suka daddale yarjejeniyar kare mabambantan halittu na MDD karo na 15 (COP15) a birnin Kunming, shi ya sa suka yi tattaki har zuwa birnin don halartar taron.
Wannan raha ce kawai, amma a hakika, a jiya ne aka kaddamar da taron na COP15 a birnin Kunming, hedkwatar lardin Yunnan. Taken taron shi ne, "Wayewar kai game da muhallin halittu: Gina makomar bai daya ga daukacin halittun dake doron duniya", kuma dalilin da ya sa aka gudanar da taron a lardin Yunnan, shi ne sabo da irin albarkatun halittun da ake da su a wurin. Lardin Yunnan ya kasance lardin da ya fi samun mabambantan halittu a fadin kasar Sin. Domin ba da kariya ga halittun yadda ya kamata, lardin Yunnan ya tsara dokokin kare mabambantan halittu, wadanda suka sa kaso 90% na yanayin halittu da ma kaso 85% na nau’o’in halittu suka samu kariya yadda ya kamata.
In mun dau misali da giwayen da muka ambata da farko, wadanda a nan kasar Sin suka barbazu kawai a sassan Xishuang Banna da Pu’er da Lincang na lardin Yunnan. Bisa kokarin da aka yi na ba su kariya, yawansu ya karu daga 150 a farkon shekarun 1980 har zuwa 300 na yanzu.
Ba ma kawai a lardin Yunnan ba, a duk fadin kasar Sin ma ana ba aikin kiyaye mabambantan halittu muhimmanci. Musamman ma a cikin shekaru 10 da suka wuce, ra’ayin nan na kiyaye muhallin halittu ya yi ta shiga zukatan jama’a sosai. Bisa ga matakan da aka dauka ciki har da kafa gandun kasa, yanzu kaso 90% na yanayin halittu na kasa da ma kaso 71% na muhimman halittun da gwamnati ke kokarin kare su suna samun kariya yadda ya kamata, har ma wasu halittun da a baya suke kokarin karewa yanzu adadinsu na karuwa.
A yau 12 ga wata, aka gudanar da taron kolin shugabanni COP15, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi a taron ta hanyar haɗin bidiyo. Inda ya ce, “Giwayen da suka doshi arewa wadanda daga baya suka koma ainihin muhallinsu a watannin da suka gabata, sun fadakar da mu a kan nasarorin da kasar Sin ta samu wajen kare halittu. Kasar Sin za ta ci gaba da mai da muhimmanci a kan kiyaye muhallin halittu, don gina kyakkyawar kasar Sin.” Ban da haka, ya kuma sanar da zuba kudin Sin yuan biliyan 1.5, don kafa asusun kare mabambantan halittu na Kunming, don kuma nuna goyon baya ga kasashe masu tasowa wajen kare mabambantan halittu.
Mabambantan halittu su ne tushen rayuwar dan Adam. An ce, taron zai tsara shirin kare mabambantan halittu bayan shekarar 2020, don haka, muna fatan taron da ake yi zai taimaka ga kiyaye makomar halittu a fadin duniya.(Lubabatu)