logo

HAUSA

’Yan bindiga sun kai hari ofishin ’yan sanda a kudancin Najeriya, tare sace ’yar sanda

2021-10-12 10:12:59 CRI

Rundunar ’yan sandan Najeriya a ranar Litinin, ta ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan wani hari da aka kai kan ofishin ’yan sanda tare da sace wata ’yar sanda a jihar Enugu da ke kudancin kasar da wasu ’yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka yi.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Enugu Daniel Ndukwe, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, sun mamaye ofishin 'yan sanda da ke karamar hukumar Uzo-Uwani na jihar Enugu, inda suka bude wuta kan jami'an tsaron da ke bakin aiki, sannan suka yi awon gaba da wata ’yar sanda a ofishin.

Ndukwe ya ce ba a san manufar maharan ba, kuma tawagogin ’yan sanda masu yaki da bata gari, ciki har da sashen binciken manyan laifuka na jihar, sun kara kaimi wajen gano ’yar sandan da aka sace tare da cafke wadanda ake zargi. (Ibrahim Yaya)