logo

HAUSA

Dukkan halittun duniya na bukatar juna domin rayuwa cikin aminci

2021-10-12 16:53:11 cri

An bude taro na 15 na bangarorin da suka sa hannu kan yarjejeniyar kare nau’o’in halittu ta MDD wato COP15 da yammacin Litinin din, a birnin Kunming, fadar mulkin lardin Yunnan, na kudu maso yammacin kasar Sin. Za a iya cewa, taron mai taken "Wayewar kai game da muhallin halittu: Gina makomar bai daya ga daukacin halittun dake doron duniya", ya zo a kan gaba, wato a yayin da ake fuskantar rashin jituwa tsakanin muhallin halittu da zamantakewar bil adama da kuma yadda wasu halittun ke fuskantar barazanar bacewa baki daya daga doron kasa.

Hakika ayyukan bil adama a fadin duniya, sun bayar da gudunmuwa wajen fuskantar tabarbarewar halittu da muhallansu, bisa la’akari da yadda ake fama da talauci da tashe-tashen hankula har ma da fafutukar neman ci gaba.

Sai dai yayin da ake neman ci gaba da kokarin inganta zamantakewa, bai kamata a manta cewa, bil adama da sauran halittu na bukatar juna domin rayuwa cikin aminci ba. Don haka, kiyaye kasancewar halittu daban-daban hakki ne da ya rataya a kan daukacin bil adama.

A matsayinta na kasar dake rajin tabbatar da jituwa tsakanin bil adama da muhalli da kuma halittu daban-daban, MDD ta yabawa kasar Sin bisa yadda ta himmantu har yawan yankunan kiyaye muhallin halittu dake sassan kasar ya kai dubu 11.8, kuma fadin yankunan gaba daya ya zarce hekta miliyan 170, wanda ya dauki kaso 18 bisa dari na fadin yankin kasar. Tabbas wannan ya nuna cewa, ba maganar fatar baki kadai Sin take yi game da batun ba, wato ta na daukar matakai a aikace wajen cimma burin samar da makomar bai daya ga daukacin halittu.

Bai kamata a rika tuya ana mantawa da albasa ba, kamar yadda na bayyana a baya, dukkan halittu na bukatar juna domin rayuwa cikin aminci, don haka, ya kamata yayin da ake neman ci gaba, a daya bangaren ya kamata a mayar da hankali wajen kare sauran halittu da muhallansu. Tuni aka fara fuskantar mummunan tasirin rashin kulawar da ake nunawa sauran halittu a duniya, kuma muddun ana son shawo kan wadancan tasiri, dole ne a dauki matakan daidaita su ta hanyar dakatar da ayyukan dake kai wa ga lalacewarsu da muhallansu.

Matakan da kasar Sin ta dauka kamar na hana kamun kifi a kogin Yangtze na tsawon shekaru 10 domin ceto halittun cikin ruwa da kafa lambunan shakatawa da kiyaye ni’imtattun wurare masu damshi da kafa dazuka da kiyaye nau’o’in halittu daban-daban da amfani da sabbin fasahohi a wannan bangare da sauransu, sun zama misalai kuma abun koyi ga kasashen duniya. Ya kamata wannan taro dake gudana, ya farkar da sauran sassan duniya, su dauki matakan da suka dace don kyautata makomar daukacin halittun dake doron duniya.