Guo Fenglian: kokarin aiki bisa aniyar inganta rayuwar al’ummar Sin
2021-10-11 15:38:40 CRI
Guo Fenglian, ita ce sakatariyar Jamniyyar Kwaminis ta kasar Sin da ke kauyen Dazhai na gundumar Xiyang ta birnin Jinzhong dake lardin Shanxi na arewacin kasar Sin, kana ‘yar majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, wadda ta kasance hukuma mafi koli ta kafa doka a kasar. Cikin shekaru 30 da suka gabata, karkashin shugabancin Guo, mutanen kauyen Dazhai sun yi aiki tukuru wajen inganta rayuwarsu. Duk da cewa tana cikin shekaru 70, Guo ba ta taba kasa a gwiwa ba, a yunkurinta na bunkasa kauyen.
Guo Fenglian, wadda ta shiga JKS shekaru 55 da suka gabata, ta fi damuwa da inganta rayuwar ‘yan uwanta mutanen kauyen Dazhai. “abu ne mai wuya samun rayuwa mai dadi. Dukkan jin dadin da muka samu, mun samu ne daga dabarun jam’iyya, ciki har da sauye-sauye da bude kofa, da kuma gomman shekarun da muka shafe muna aiki tukuru. Don haka, bai kamata a yi asarar ruhin Dazhai na dogaro da kai da fafutuka ba. Dazhai zai ci gaba da bin jam’iyya da hanyar gurguzu mai sigar kasar Sin”.
Rayuwar Guo kamar littafi take, da shafuna cike da bayanai na irin namijin kokarinta. A lokacin da take shekara 16, Dazhai ta aiwatar da noman hadaka. Karkashin shugabancin Chen Yonggui, sakataren jam’iyya na kauyen a wancan lokaci, mutanen kauyen suka shawo kan kalubale ta hanyar jarumta. Sun yi aiki ba dare ba rana, ba tare da la’akari da samun kudin aikin ba, wajen gina kunyoyi da tona hanyoyin ban ruwa.
“A wancan lokaci, na kan tashi da karfe 5 na kowacce safiya domin tattara duwatsun dake gefen tsaunika. Daga bisani, na kan debo kasa kuma a hankali a hankali nake gina kunyoyi.”
Guo ta tuna cewa, irin yawan amfanin gona da aka samu a wajen da ba shi da kasar noma a farkon shekarar 1960, ya zama tamkar al’ajabi a fannin raya aikin gona. An dauki kauyen Dazhai a matsayin jagora kuma abin misali ga sauran sassan kasar Sin a fannin raya aikin gona.
Saboda kwazonta, Guo ta zama jagorar matasa a kauyen. Ta shiga JKS ne a watan Junairun 1966. Daga bisani ta yi fice a matsayin tauraruwa a lokacin da ake koyon dabaru daga aikin gona irin na Dazhai, da ya yi fice a kasar.
Guo ta rike mukamai da dama a wajen kauyen bayan shekarar 1980. A shekarar 1991, bayan ta gano an bar kauyen a baya a manufar gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje, ba tare da bata lokaci ba, Guo ta koma kauyen. Nan da nan ta kara zama jagora a matsayin sakatariyar jam’iyya ta kauyen, haka kuma Janar manajan kamfanin raya tattalin arziki na Dazhai.
Karkashin shugabancinta, kauyen ya fara gina kamfanonin saka tufafi da na siminti da ababen sha da raya aikin gona da kiwo da yawon bude ido da tashoshin raba kwal. Kayayyakin da aka yi wa lakabi da “Dazhai” kamar ruwan tsami da fulawa da hatsi, sun samu karbuwa a kasuwa.
A shekarun baya-bayan nan, kauyen ya mayar da hankali wajen kare muhalli. Ya tsara tare da aiwatar da wani sabon shirin raya tattalin arziki, inda kayayyakin gona da yawon bude ido da saka tufafi, suka kasance ginshikin kasuwancinsa.
Jimilar kudin shigar harkokin kasuwanci na Dazhai ya kai Yuan miliyan 460, kwatankwacin dala miliyan 71, a shekarar 2019. Baya ga haka, adadin kudin shigar ko wanne mutumin kauyen, ya kai Yuan 23,000, kwatankwacin dala 3,538. Dazhai da ya taba yin fice ya sake haskawa, inda yake jan hankalin masu ziyara da yawon bude ido kusan 500,000 a kowace shekara.
Da ta yi waiwaye, Guo ta yi farin cikin cewa, kwalliya ta biya kudin sabulu. Ta yi imanin cewa, Dazhai na yanzu, ya zarce tunanin mutane. “Kauyen ya samu manyan sauye-sauye, wadanda babu wanda ya taba tsammani,” cewar Guo.
Ta ci gaba da zurfafa gyare-gyare a Dazhai, musamman wadanda suka shafi bunkasa dabarun raya kauyen. Burin Guo a yanzu shi ne, sauya Dazhai zuwa fitaccen tambari a matsayin wurin yawon bude ido mai kiyaye muhalli. “Za mu so a ce ba tarihin Dazhai kadai baki suka sani ba, wato su san kauyen na yanzu da kuma na nan gaba, wato kauyen da ya ci gaba a sabon zamani, inda dukkan mutane ke more hakkokinsu na ilimi da kiwon lafiya da kula da tsoffi’’.
Ba tabbatar da ci gaban Dazhai kadai Guo ta yi ba, har da mayar da hankali kan raya kauyuka makwabta, ciki har da taimaka musu yaki da fatara. Ta yi amfani da dabarun da suka amfanawa Dazhai wajen raya harkar yawon bude ido, domin taimakawa kauyukan dake gundumar Xiyang raya masana’antar yawon bude ido.
‘Yar kasuwa Ma Huailan tare da mai gidanta Zhou Yinzhu, sun koma garinsu Jinggou, wani kauye dake birnin Sandu, bayan an yi musu maganin cutar daji.
Ba za su iya jure talaucin dake kauyensu ba, don haka suka shirya zuba jari da kudin da suka dade sun tarawa, domin taimakawa kauyen fatattakar talauci.
A shekarar 2005, aka zabi Ma a matsayin daraktar kwamitin jam’iyya ta kauyen Jinggou, saboda aminci da burin da mutanen kauyen ke da shi. Ma ta ziyarci Guo, tana mai fatan samun shawarwari.
Guo ta yi farin ciki da irin kaunar da Ma da mijinta ke wa kauyensu. Bayan ta fahimci yanayin da Jinggou ke ciki, Guo ta ziyarci kauyen, inda ta hada hannu da mutanen kauyen domin lalubo hanyoyin kara musu kudin shiga
Guo ta samo dabarar, wato “kauyuka masu wadata su taimakawa matalautan kauyuka”, kuma ta bada shawarar Dazhai da Jinggou su hada kai wajen yaki da talauci. Ta yi wa Jingguo lakabi da “Dazhai na biyu” kuma ta yi aiki a matsayin sakatariyar Jam’iyya na kauyukan biyu a lokaci guda.
Cikin shekarun da suka gabata, ayyukan inganta rayuwar jama’a da samar da ci gaba sun samu wajen zama a Jingguo. Kauyen wanda a baya ya yi fama da talauci, ya zama fitaccen abun koyi. Kudin shigar kowanne mutumin kauyen ya karu daga kasa da Yuan 700, kwatankwacin dala 108 kafin shekarar 2006, zuwa sama da Yuan 5,000, kwatankwacin dala 769, a shekarar 2013.
Taimakon Guo bai tsaya kadai ga kauyenta da makwabtansa ba. Ta kuma gabatar da shawarwari ga kungiyar raya kauyuka ta kasar Sin, domin taimakawa kauyen Jingangtai da ya yi fama da talauci a baya.
“Manoma a duk fadin kasar nan ‘yan uwan juna ne, dole ne mu yi amfani da tasirin fitattun kauyuka wajen taimakawa matalautan kauyuka,” cewar Guo.
Cikin shekaru kalilan, Jingangtai ya samu tagomashi. A ranar 29 ga watan Afrilun 2020, lardin Anhui ya sanar da labari mai dadi cewa, an cire gundumar Jinzhai da kauyen Jingangtai ke karkashinta, daga jerin yankunan kasar Sin masu fama da talauci.
“Sai mun dage za mu iya fatattakar talauci daga tushe,” cewar Guo. “hanyar da manoma za su bi su yaki talauci su samu wadata, na da wahalar gaske. Dazhai ba zai taba mantawa da tarihinsa ba….hakkin mu ne taimakawa yankunan karkara da manoma samun ci gaba.”
An zabi Guo a matsayi ‘yar majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ce lokacin da take da shekara 24. An sake zabarta sau dama. Yanzu, wakiliya ce a majalisar karo na 13. “wannan shi ne amincin da Jam’iyya da jama’a ke da shi a kai na. Abun alfahari ne, kana hakki ne da ya rataya a wuyana,” cewar Guo. Ta kara da cewa, saboda ta rayu a karkara, za ta ci gaba da tsayawa manoma, muddin akwai bukatar hakan.(Kande Gao)