logo

HAUSA

Shugaba Xi ya jajantawa takwaransa na Rasha bisa aukuwar hadarin jirgin fasinjan kasar

2021-10-11 20:36:01 CRI

Shugaba Xi ya jajantawa takwaransa na Rasha bisa aukuwar hadarin jirgin fasinjan kasar_fororder_4afbfbedab64034f636700500cf539380b551df9

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jajantawa takwaransa na Rasha Vladimir Putin, bisa aukuwar hadarin jirgin fasinjan kasar a Tatarstan, hadarin da ya haifar da asarar rayuka da dama.

Cikin sakon wanda shugaba Xi ya mika ga gwamnatin Rasha a Litinin din nan, ya ce ya kadu da jin labarin aukuwar hadarin, yana mai mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu, da kuma fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.  (Saminu)