logo

HAUSA

Gaskiya Ba Ta Bukatar Ado

2021-10-11 16:33:59 cri

Gaskiya Ba Ta Bukatar Ado_fororder_微信图片_20211011160159

Hakika ita gaskiya dai daya ce kuma daga kin gaskiya sai ba ta in ji ’yan magana. A lokuta da dama, gwamnatin Sin ta sha bayyana manufofinta na diflomasiyya da matsayinta game da batun dake shafar cudanya a matakan kasa da kasa da na shiyya cewa, babban burinta shi ne kokarin tabbatar da ci gaban bil adama ba tare da cin zarafi ko muzgunawa ko kuma yin shisshigi a harkokin cikin gidan wata kasa ko shiyya ba. Har kullum burin gwamnatin Beijing shi ne, gina makomar bil adama ta bai daya, domin a gudu tare a tsira tare. To sai dai duk da aniyar da take da shi na kokarin gina alkhairai ga al’ummar duniya, hakan bai hana wasu kasashen yammacin duniya sukarta ba, da yi mata yarfe, gami da kokarin shafawa kasar kashin kaza kan batutuwa daban daban, da ma an ce dokin mai baki ya fi gudu. To amma dai sannu a hankali gaskiya za ta yi halinta. Ko da a karshen wannan mako, wani masanin kasar Birtaniya ya fasa kwai, inda ya bayyana abin da yake ransa game da irin tasa mahangar inda ya ce, yadda kasar Sin take kokarin tabbatar da ci gaban al’umma na bai daya ya nuna yadda take sauke nauyin dake bisa wuyanta wanda kasashen yamma suka kasa yi. Martin Jacques, wani sanannen masanin kasar Birtaniya ne, ya bayyana yayin wata tattaunawa a kwanan nan cewa, duk da yadda kasashen yammacin duniya, musamman Amurka, suke ci gaba da yayata batun matsalolin dake kawo baraka a harkar tattalin arzikin duniya, sai dai wadannan kasashen sun gaza taka rawar a zo a gani don sauke nauyin da ya dace su sauke wajen warware wadannan matsalolin. Amma sabanin hakan a cewar masanin, kasar Sin tana kokarin bin hanyoyin warware matsalar rashin daidaito ta hanyar kyautata tsarin samar da makoma ta bai daya ga dukkan bil adama. Martin Jacques ya ce, kasar Sin tana yin abubuwan da ya kamata a ce kasashen yamma ne ke yinsu, amma abin takaice sun gaza a maimakon hakan sun bar jaki suna bugun teki, sai yawan surutai na babu gaira babu dalili. Dama dai an ce kifi na ganinka mai jar koma. (Ahmad Fagam)