Ya kamata kasashen dake ikirarin fafutukar kare hakkin dan Adam su gaggauta gyara kura-kuransu
2021-10-11 21:31:24 CRI
Kwanan nan ne aka rufe taro karo na 48, na kwamitin kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya, inda a cikin tsawon wata daya, kasashe da dama suka zargi kasashen Amurka, da Birtaniya, da Kanada, da Australiya, saboda munanan laifuffukan da suka aikata, gami da manufofin rashin gaskiya da suke aiwatarwa a fannin hakkin dan Adam. Kuma a wajen bikin rufe taron, an zartas da kudurin da kasar Sin ta fitar, dangane da illolin dake tattare da more hakkin dan Adam, da wasu matsalolin tarihi sakamakon mulkin mallaka suka haifar, al’amarin da ya shaida cewa, kasa da kasa sun kara fahimtar ainihin manufofin kasashen yammacin duniya, wato nuna babakere bisa hujjar kare hakkin dan Adam, kana, da yin shisshigi cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe bisa hujjar tabbatar da tsarin demokuradiyya.
Kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD, wani muhimmin dandali ne da bangarori daban-daban suke amfani da shi, wajen gudanar da shawarwari da hadin-gwiwa a fannin kare hakkin dan Adam, amma akwai wasu kasashen yamma, wadanda ke yunkurin mayar da shi a matsayin wani wurin da suke yin fito-na-fito a fannin siyasa, da shafa wa kasar Sin bakin fenti kan batutuwan da suka shafi Xinjiang da Hong Kong. Amma malam Bahaushe kan ce, karya fure take, ba ta ‘ya ‘ya. A wajen taron da aka yi a wannan karo, akwai kasashe kusan 100 da suka goyi bayan kasar Sin, inda suka jaddada cewa, harkokin da suka jibanci Xinjiang, da Hong Kong da Tibet, harkoki ne na cikin gidan kasar Sin zalla, bai kamata sauran kasashe su tsoma baki a ciki ba.
Kasar Sin ta dade tana namijin kokarinta wajen kare hakkokin dan Adam, abun da ba kare hakkokin ‘yan kasar kawai ya yi ba, har ma ya taimaka sosai ga ci gaban harkokin kare hakkin dan Adam na duk fadin duniya baki daya. Ya dace, wadannan kasashen da suke ikirarin cewa wai su ne masu fafutukar kare hakkin dan Adam, su gyara kura-kuran da suka aikata, da dakatar da nuna yatsa ga sauran kasashe a fannin kare hakkin dan Adam. (Murtala Zhang)