logo

HAUSA

UNICEF ta shirya shawo kan sabuwar barkewar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

2021-10-10 16:30:09 CRI

UNICEF ta shirya shawo kan sabuwar barkewar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo_fororder_d4628535e5dde711817121c74340f3129c16619c

Asusun kula da kananan yara na MDD UNICEF, ya bayyana cewa, yana aiki da hukumomin lafiya a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, bayan samun rahoton sabuwar barkewar cutar Ebola a arewa maso gabashin kasar.

Gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, ta tabbatar da yammacin ranar Juma’a cewa, wani yaro mai shekaru 3 ya rasu sanadiyyar cutar Ebola a ranar 6 ga wata, a yankin Beni dake arewa maso gabashin lardin Kivu ta Arewa, daya daga cikin inda aka fara samun barkewar cutar ta karshe da aka dakile ta a ranar 3 ga watan Mayun bana.

Wata sanarwar da asusun UNICEF din ya fitar, ta ruwaito cewa, tuni jami’ansa suka shiryawa tunkarar cutar. Kana karin jami’ai za su tafi Beni domin bada tallafi na farko kuma mafi muhimmanci ta hanyar wayar da kan al’umma da ayyukan kashewa da dakile kwayar cutar.   

Mutane 12 ne suka kamu yayin da 6 suka mutu, biyo bayan barkewar Ebola a farkon bana, wadda ta shafe kusan watanni 3, a yankunan Biena da Katwa da Musienene da Butembo na lardin Kivu ta arewa. (Fa’iza Mustapha)