logo

HAUSA

Kamata ya yi a amince da kasancewar ra’ayoyi daban-daban a duniya

2021-10-10 18:39:24 CRI

图片默认标题_fororder_微信图片_20211010183613

Daga Amina Xu

A makon jiya na rubuta wani sharhi mai taken “Kamata Ya Yi A Kalli Hakikanin Halin Da Sin Ke Ciki” a shafin FACEBOOK, inda na bayyana cewa, na taba jagorantar wata tawagar manyan wakilan kafofin yada labarai na kasar Najeriya da su ziyarci kasar Sin, don kallon hakikanin halin da Sin ke ciki, matakin da ya kyautata matsayinsu kan kasar Sin wanda wasu kafofin yada labarai na kasashen yamma ke kokarin mallake matsayinsu kan kasar Sin. Wadannan manyan wakilai sun rubuta hakikanin halin da suka gani a kasar Sin ta kafofinsu. Masu amfani da Intanet da yawa sun bayyana cewa, Sin na bukatar al’ummar duniya su fahimce ta. Amma, daga cikinsu akwai wani mai suna Auwalu Wisdom Bichi ya ce, an bar wadannan ‘yan jarida sun sanar da al’ummarmu hakikanin halin da Sin ke ciki, daga nan kun kawar da farfaganda. Abin bacin rai shi ne, ‘yan Afrika da dama sun dauki irin wannan matsayi cewa, Sin tana yin farfaganda. Saboda wasu kafofin yada labarai na kasashen yamma suna yunkurin bata sunan kasar Sin, har sun sa mutane irinsu Auwalu Wisdom Bichi kasa fahimtar kasar Sin yadda ya kamata.

Lokacin da nake aiki a Najeriya, na taba haduwa da wani dan Najeriya wanda ya yi fushi sosai ya nuna min wani labari cewa, don me kuke cin zarafin musulmai? Wani labari na bogi ne ya nuna mana, wai an hana musulmai a Sin yin azumi. Na gayya masa cewa, hakikanin hali shi ne wadannan mutane suna bayyana rashin jin dadin su ta hanyar daina cin abinci a lokaci da ba na azumi ba, don haka aka mika musu abinci don kada su ji yunwa. Kowace kasa na iya fuskantar faruwar irin wannan abu, ciki har da Najeriya. Har na nuna masa hoton bidiyo dake bayyana hakikanin abin da ya faru kan wannan batu, amma ya ce, wannan labari na bogi ne da kasar Sin ta kirkiro don kawar da laifinta. Na tambaye shi cewa, ko ka iya tabbata labarin da ya duba na bogi ne ko a'a? Amma ya ki yarda da labarin da Sin ta bayar duk da cewa na gabatar masa da shaidu. Don haka, na yi niyyar taimakawa kafofin yada labarai na Najeriya wajen samun karin fahimtar kasar Sin, hakan ya sa na shiga aikin gayyatar manyan wakilan kafofin yada labarai na Najeriya da su ziyarci kasar Sin da ma ingiza hadin kan kafofin yada labaran Sin da Najeriya. Saboda a ganina, wasu kasashen yamma sun samu arziki ta hanyar yin mulkin mallakar sauran kasashe, hakan sun yi gaba a duniya a fannin tattalin arziki da kimiyya da al’adu, a yayin da kasashe marasa karfi ba su iya bayyana ra’ayinsu a duniya, saboda hakan, kafofin yada labarai na kasashen yamma sun dade suna mallakar dandalin yada labarai a duniya. Karya za ta zama gaskiya saboda maimaitawa da aka yi. Yanzu Sin tana samun bunkasuwa mai sauri bayan gwagwarmayya da take yi ta dogaro da kanta, har ma an fara jin muryar kasashe masu tasowa a duniya, abin mai kyau ne. Amma, wasu kafofin yada labarai na kasashen yamma ba su son ganin haka, suna tsoron jin mabambanta ra’ayoyi a duniya. Kowa ya gani, cimma demokuradiyya da ‘yanci na da mabambanta hanyoyi, idan wasu kasashe sun bayyana ma’anar demokuradiyya da ‘yanci bisa ra’ayinsu, to wa zai iya karyata su? Idan su kadai suna iya bayyana ra'ayinsu, to za su rufe idanuwa da kunnuwa da tunaninku, suna gabatar muku abubuwan da suke son ku gani, shin ko wannan ya bayyana demokuradiyya da ‘yanci?

Mataimakin darektan ofishin nazarin tattalin arzikin duniya da dangantakar kasa da kasa na kwalejin kimiyya da fasaha na kasar Rasha Alexander Romanov ya taba bayyana cewa, kasashen yamma su kan yi ikirari cewa, sun yi gaba a fannin demokuradiyya da‘yanci, amma a hakika dai wasu kafofin yada labarai na kasashen yamma ba su bayyana demokuradiyya da 'yanci kan batutuwan dake shafar kasar Sin, saboda a karkashin yanayin siyasarsu, zargi da kuma bata sunan kasar Sin abin da‘yan siyasar suke so ne, idan ba su yi haka ba, za a yanke kudaden da za a samar musu ko korar su daga mukaminsu. Yada jita-jita don bata sunan kasar Sin ba abin da jama’ar wasu kasashen yamma suke so ba ne, amma manufofi ne na wasu 'yan siyasar kasashen yamma.

Ina son in gayawa Auwalu Wisdom Bichi da sauran mutanen dake daukar ra’ayi irinsa daya cewa, duniya da muke ciki na kunshe da ra’ayoyi da al’adu da dama, bai kamata muryoyin wasu kasashen yamma ne kawai ake ji a duniya, ya kamata kasashe daban-daban su samu damar bayyana ra’ayoyinsu. Ra’ayin wasu kafofin yada labarai na kasashen yamma ba su iya wakiltar daukacin duniya, ya kamata duniya ta saurari ra’ayin kasar Sin, wannan ba farfaganda take yi ba, wannan shi ne hakkin bayyana ra’ayin kanta. (Amina Xu)