logo

HAUSA

Xi: Dole ne a kammala aikin tabbatar da cikakkiyar hadewar kasar Sin

2021-10-09 20:38:24 CRI

Xi: Dole ne a kammala aikin tabbatar da cikakkiyar hadewar kasar Sin_fororder_sin

“Wajibi ne a kammala aikin cikakkiyar hadewar kasar Sin, kuma tabbas ne za a cimma wannan buri!" A yayin taron bikin tunawa da cika shekaru 110 da juyin juya halin Xinhai a ranar 9 ga wannan wata, shugaban kasar Xi Jinping, ya bayyana hakan cikin muhimmin jawabin da ya gabatar, inda ya jaddada aniyar kare ikon kasa da tabbtar da cikakkun yankunanta.

Shugaban ya ce tilas ne kasar Sin ta zama dunkulalliya. Wannan wata bukata ce da ake da ita ba tare da zabi ba, don tabbatar da farfadowar kasar Sin a sabon zamanin da muke ciki. "Batun ‘yancin kai na Taiwan" wannan wani tsohon batu ne da ya zama tarihi kuma ya riga ya wuce sai tarihinsa. Wadanda suke neman bijirewa kasar, kuma suke kokarin kawo baraka a kasa ba za su taba wanyewa lafiya ba. Duk wani yunkuri daga kasashen ketare na neman tsokana kan batun yankin Taiwan, ko shakka babu illar hakan za ta koma kan su.(Ahmad)