logo

HAUSA

Ya dace Sin da Japan su yi aiki tare domin ingiza huldar da ta dace da bukatun sabon zamani

2021-10-09 16:11:56 CRI

Ya dace Sin da Japan su yi aiki tare domin ingiza huldar da ta dace da bukatun sabon zamani_fororder_sin-japan

Jiya Juma’a 8 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta da firaministan kasar Japan Fumio Kisida ta wayar tarho, inda ya jinjinawa sabuwar gwamnatin Japan saboda ta mai da hankali kan huldar dake tsakaninta da kasar Sin, kana ya nuna cewa, kasarsa ita ma tana son kara karfafa hadin gwiwa dake tsakaninta da Japan. Fumio Kisida shi ma ya bayyana cewa, a halin yanzu huldar dake tsakanin Japan da Sin ta riga ta shiga sabon zamani.

Ana ganin cewa, zantawarsu tana da babbar ma’ana, inda shugaba Xi ya gabatar da cewa, ya dace a bi ka’idoji daban daban da aka tanada a cikin takardun siyasa hudu da kasashen biyu suka daddale, ta yadda za su tabbatar da matsayar siyasa da suka cimma wato gudanar da hadin gwiwa a maimakon kawowa juna kalubale, a sa’i daya kuma, ya kamata sassan biyu su kara karfafa cudanya wajen gudanar da harkokin kasa da manufofin tattalin arziki, ta yadda za su kare muhallin cinikayya da zuba jari mai adalci ba tare da rufa rufa ba, kana dole ne sassan biyu su nace kan manufar gudanar da harkokin kasa da kasa tsakanin bangarori daban daban, ta yadda za su kiyaye ci gaban duniya cikin lumana. Ana iya cewa, dabarun da shugaba Xi ya gabatar sun ba da jagoranci ga aikin kafa huldar da ta dace da bukatun sabon zamani dake tsakanin Sin da Japan (Jamila)