‘Yan sandan Najeriya sun sha alwashin tsaurara tsaro a makarantun arewa maso yammacin kasar
2021-10-09 17:07:38 CMG
Hukumar ‘yan sanda a Najeriya ta yi alkawarin daukar matakan tsaurara tsaro a makarantun jahar Zamfara dake shiyyar arewa maso yammacin kasar.
Ayuba Elkanah, kwamishinan ‘yan sandan jahar Zamfara, ya bayyana hakan yayin wata ziyara da ya kai a wasu makarantun ilmi dake Gusau, babban birnin jahar, a matsayin wani mataki na tabbatar da tsaro a makarantun dake fadin jahar.
Elkanah ya ce, ziyarar na zuwa ne a matsayin wani bangare na kokarin da jami’an ‘yan sandan ke yi don magance kalubalolin tsaro dake addabar jahar da nufin tabbatar da baiwa makarantun jahar tsaro da kariya, musamman makarantun gaba da sakandare wadanda a halin yanzu suke cikin zangon karatunsu.
Jami’in ya ce, makasudin ziyarar tasa shi ne domin duba yanayin tsare tsaren harkokin tsaron makarantun jahar da nufin sake tsara dabarun tabbatar da tsaron dalibai da makarantun dake yankunan jahar.(Ahmad)