logo

HAUSA

Xi ya ce za a iya warware batun Taiwan bayan da ci gaban kasa ya tabbata

2021-10-09 17:03:25 CMG

Xi ya ce za a iya warware batun Taiwan bayan da ci gaban kasa ya tabbata_fororder_1009-xi-Taiwan-Ahmad

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yau Asabar cewa, batun tambayoyin dake tasowa na tada jijiyar wuya game da batun yankin  Taiwan na kasar Sin, batu ne za a iya warware shi bayan da ci gaban kasar ya tabbata.

Da yake jawabi a taron bikin cika shekaru 110 bayan juyin juya halin kasa na shekarar 1911, babban sakataren kwamitin tsakiyar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin koli na sojojin kasar, Xi Jinping, ya bayyana cewa, wannan batu ya ta’allaka ne da irin jajircewar da aka nuna a bisa tarihin kasar Sin, amma abu mafi muhimmanci shi ne, wannan batu ne dake shafar dukkan al’ummun Sinawa.

Shugaba Xi ya ce, sake tabbatar da hadin kan kasa ta hanyar lumana shi ne babban burin dukkan al’ummar Sinawa, wanda ya kunshi har da al’ummar yankin Taiwan.(Ahmad)

Ahmad