logo

HAUSA

Yan bindiga sun kashe mutane 10 yayin wani hari a arewa maso yammacin Najeriya

2021-10-08 11:25:58 CRI

Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kashe mutanen kauye 10 tare da raunata wasu 11 yayin hari da suka kaddamar a yankin jahar Katsina dake shiyyar arewa maso yammacin Najeriya, kakakin hukumar ’yan sandan jahar ya tabbatar da faruwar lamarin.

Gambo Isah, kakakin hukumar ’yan sandan jahar Katsina, ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho cewa, maharan wasu ’yan bindiga ne, inda suka kaddamar da harin da yammacin ranar Talata a kauyen Yasore dake karamar hukumar Batsari a jahar.

A cewar Isah, binciken da ’yan sanda suka gudanar kawo yanzu ya gano cewa, harin ramuwar gayya ne da ’yan bindigar suka kaddamar, inda ake zargin wasu ’yan kungiyar sindiri na yankin wanda gwamnatin jahar ta jima da haramta kungiyar sun kaddamar da hari kan mambobinsu har ma sun kashe wasu daga cikin ’yan bindigar.

Harin na ranar Talata ya dauki tsawo sa’o’i da dama, yayin da ’yan bindigar kan babura sama da guda 20 dauke da makamai irin na zamani suka mamaye kauyen, kamar yadda kafafen yada labarai suka rawaito daga wasu shaidun gani da ido.

Mazauna yankin sun ce ’yan bindigar sun shiga gidaje, sun sace dabbobi, da kwace kudade, da wayoyin hannu, da tufafi da kuma kayan abinci na mazauna kauyen a yayin da suka kai harin. (Ahmad)