logo

HAUSA

Shugaban kasar Najeriya ya kare matsayin gwamnatinsa na shirin karbar rance don bunkasa tattalin arzikin kasar

2021-10-08 11:19:30 CRI

Shugaban kasar Najeriya ya kare matsayin gwamnatinsa na shirin karbar rance don bunkasa tattalin arzikin kasar_fororder_211008-NW Nigeria-Ahmad

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya kare matsayin gwamnatinsa game da shirin karbar bashi don cike gibin kasafin kudin kasar na shekarar 2022, inda ya bayyana dalilansa cewa, zai yi hakan ne da nufin tallafawa bunkasar tattalin arziki da kuma daidaituwar yanayin tattalin arzikin kasar.

Shugaba Buhari, yayin da yake gabatar da kudirin kasafin kudin kasar na shekarar 2022 wanda ya kai naira triliyan 16.39 kwatankwacin dala biliyan 39.9 a taron hadin gwiwa na majalisun dokokin kasar biyu a Abuja, ya bayyana cewa wasu masu suka sun bayyana damuwa game da aniyar gwamnatinsa na nemaan ciyo bashi da nufin cike gibin kasafin kudin kasar na badi.

Shugaban Najeriyar ya ce, masu sukar suna da ikon bayyana damuwarsu. Sai dai, a cewarsa, matakin kudaden da gwamnatin tarayyar kasar ta ranto bai wuce mizani ba. Za a yi amfani da kudaden rancen ne wajen aiwatar da wasu muhimman ayyuka kuma za a bayyanawa al’umma a bayyane.

Yayin da kasar ta tsara kasafin kudinta na shekarar 2022 wanda ya kai naira triliyan 16.39, Najeriyar tana bukatar kudi naira triliyan 6.26 domin cike gibin kasafin kudin, wanda ya kai matakain GDPn kasar da kashi 3.39%, wanda ya zarta kashi 3% bisa ga dokar tsara kasafin kudi ta shekarar 2007.

Haka zalika, shugaban majalisar dattijan Najeriya Ahmad Lawan, ya koka game da gibin da aka samu a kudirin kasafin kudin kasar na shekarar 2022, duk da kasancewar gibin ya ragu da kashi 4.52% na GDPn kasar, idan an kwatanta da kasafin kudin shekarar 2021 wanda ya kai naira triliyan 6.45. Ya yi kira ga dukkan bangarorin majalisun dokokin kasar da bangaren zartaswa da su yi aiki tare domin rage gibin kasafin kudin ta hanyar lura da yanayin kudaden shigar da kasar ke samu. Kana ya sake yin kira ga gwamnatin tarayya da ta yi kokarin neman wasu hanyoyin samun kudaden shigarta. (Ahmad)