logo

HAUSA

Dakarun tsaron Najeriya sun ceto mutane 187 daga masu garkuwa da mutane a Zamfara

2021-10-08 19:27:24 CRI

Dakarun tsaron Najeriya sun yi nasarar ceto mutane 187, daga hannun masu garkuwa da mutane a jihar Zamfara dake shiyyar arewa maso yammacin kasar.

Da yake tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua, kakakin rundunar ‘yan sandan kasar reshen jihar ta Zamfara Muhammad Shehu, ya ce mutanen da aka sato daga sassan jihar, da ma makwafciyar ta jihar Sokoto, sun samu kubuta ne a jiya Alhamis, bayan da jami’an tsaro suka kai sumame tungar wasu masu garkuwa da mutane a dajin Tsibiri, na karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.  (Saminu)