logo

HAUSA

Takardar bayani da aka fitar ta yi fashin baki game da gudummawar Sin a fannin kare nau’o’in halittu mabambanta

2021-10-08 20:35:04 CRI

Takardar bayani da aka fitar ta yi fashin baki game da gudummawar Sin a fannin kare nau’o’in halittu mabambanta_fororder_halittu

A yau Juma’a ne gwamnatin kasar Sin ta fitar da wata takardar bayani, mai kunshe da fashin baki don gane da yadda kasar ta yi namijin kokari, a fannin kare nau’o’in halittu mabambanta.

Wannan ne dai karon farko da kasar ta fitar da irin wannan takarda, wadda ta fayyace ma’anar aikin, da manyan matakai da ake aiwatarwa, da nasarorin da kasar ta cimma, tare da gudummawar ta a fannin ga sassan kasa da kasa.

Kare nau’o’in halittu mabambanta muhimmin jigo ne na inganta rayuwar bil adama da ma ci gaban sa. Don haka ne ma kasar Sin har kullum, ke dora muhimmancin gaske ga batun kare nau’o’in halittu mabambanta. Inda a shekaru 10 na baya bayan nan, Sin ta kara azama wajen aiwatar da manufofin kare muhallin halittu, da wanzar da ci gaba ta amfani da abubuwa marasa gurbata muhalli, ta yadda fannin kare nau’o’in halittu mabambanta ya shiga wani sabon mataki a kasar.

A wannan gaba da Sin ke karbar bakuncin taron karawa juna sani, na sassan da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kare nau’o’in halittu mabambanta karo na 15, kasar za ta yi amfani da wannan dama wajen ingiza sassan masu ruwa da tsaki, ta yadda za su sake kara azama ga jagorancin ayyuka masu nasaba da kare nau’o’in halittu mabambanta. (Mai fassarawa: Saminu daga CRI Hausa)