logo

HAUSA

Sin na ci gaba da taka rawar gani a fannin samar da rigakafin cutar COVID-19 ga duniya

2021-10-07 20:44:13 CRI

Sin na ci gaba da taka rawar gani a fannin samar da rigakafin cutar COVID-19 ga duniya_fororder_a

Yayin da duniya ke ci gaba da fuskantar kalubalen da cutar COVID-19 ta haifar ga fannonin kiwon lafiya da tattalin arziki da zamantakewa, har yanzu masu fashin baki na ci gaba da kiraye kirayen samar da daidaito a fannin rarraba rigakafin cutar ga sassan kasa da kasa, ta yadda hakan zai ba da damar gaggauta dakile ci gaban bazuwar wannan annoba cikin hanzari.

Tuni dai wannan annoba ta yiwa duniya “kamun kazar kuku”, kuma mummunan tasirin ta ya bazu a dukkanin sassan kasashen duniya kanana da manya. Wani abun jan hakali ma shi ne, yadda annobar COVID-19 ta fallasa raunin wasu daga manyan kasashen duniya a fannin tunkarar ayyukan gaggawa na lafiyar bil Adama. Alal misali, a baya bayan nan adadin mutanen da cutar ta hallaka a Amurka kadai ya haura mutum 700,000. Baya ga dubban al’ummun kasar da shuka yi jinyar ta. Kana ta haifar da tarin hasarori a fannin tattalin arziki ga kasar.

Kawo yanzu dai, masana a fannin kimiyya na ci gaba da jan hankalin sassan kasa da kasa, game da muhimmancin gaggauta samar da isassun alluran rigakafin wannan annoba, a matsayin hanya daya tilo ta cin lagon annobar baki daya.

Kan haka ne kuma, sassa da dama ke ci gaba da jinjinawa kasar Sin, bisa yadda take ci gaba da samar da tallafin rigakafin ga kasashen duniya daban daban, musamman ma kasashe masu tasowa.

Kawo yanzu, kasar Sin ta samar da rigakafi sama da biliyan 1.2 ga kasashen duniya sama da 100, wanda hakan ya sanya ta zama kasa dake sahun gaba a duniya, a fannin samar da rigakafin cutar ta COVID-19.

Kaza lika, kari kan tallafin rigakafin cutar da darajar su ta kai dalar Amurka miliyan 100, Sin ta sha alwashin samar da tallafin wasu rigakafin har miliyan 100 ga kasashe masu tasowa nan da karshen shekarar bana, karkashin shirin nan na COVAX.

Idan ba a manta ba, kafin samar da rigakafin cutar COVID-19, Sin ta rarraba kayayyakin kula da lafiya, da na kandagarkin bazuwar cutar ga sassan duniya daban daban, a lokacin da duniya ke yunkurin dakile yaduwarta cikin hanzari, wanda hakan ya sanya masharhanta da dama, ke kallo kasar ta Sin a matsayin “zakaran gwajin dafi” wajen yaki da cutar COVID-19 tsakanin kasashen duniya baki daya. (Saminu Alhassan)