logo

HAUSA

Jaridar Ghanian Times ta wallafa makalar dake jinjinawa kwazon Sin a fannin yaki da cutar COVID-19

2021-10-07 15:40:13 CRI

Jaridar Ghanian Times ta wallafa makalar dake jinjinawa kwazon Sin a fannin yaki da cutar COVID-19_fororder_ghana

Jaridar Ghanian Times mallakin gwamnatin kasar Ghana, ta wallafa wata makala mai take “Salon yaki da annoba domin ceton rayuwa, kiwon lafiya da bunkasa tattalin arziki”, wadda a cikin ta aka yi bitar irin namijin kokarin da kasar Sin ta yi a fannin yaki da cutar COVID-19.

Makalar ta kuma yi karin haske game da yadda gwamnatin Sin, ke maida hankali ga maida rayuwar al’umma, da kiwon lafiyar su gaban komai, da yadda mahukuntan kasar suka tsara, tare da hade dabarun kandagarki da na shawo kan annobar, da fannin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma wuri guda.

Har ila yau, makalar ta yi fashin baki game da yadda annobar ta bude wasu sabbin damammaki, da fadada bukatun hajojin kasar Sin, da ingiza hadin gwiwa a fannin kara bude kofofin kasar. Jaridar ta ce bisa mahangar kasar, Sin ta riga ta shirya hanyar yaki da annobar da ka iya bulla.

Daga nan sai makalar ta jinjinawa kasar Sin, a matsayin ta na kasa mai yawan al’umma har sama da biliyan 1.4, wadda kuma ta kai ga kange al’ummar ta daga barazanar annobar, ta kuma shige gaba wajen sake bude ayyuka da sarrafa hajoji, ta kuma ba da gagarumar gudummawa a fannin yaki da cutar a matakin kasa da kasa.

Bugu da kari, makalar ta ce, Sin na goyon bayan hadin gwiwar kasa da kasa a yakin da ake yi da COVID-19, da gina al’ummar duniya mai managarcin tsarin kiwon lafiya, tare da samar da karin damammaki ga duniya, na cin gajiya daga sabbin nasarorin kasar.   (Saminu)