logo

HAUSA

Ya kamata Amurka ta dauki mataki domin tabbatar da matsayar da shugabanin Sin da Amurka suka cimma

2021-10-07 20:30:55 CRI

Ya kamata Amurka ta dauki mataki domin tabbatar da matsayar da shugabanin Sin da Amurka suka cimma_fororder_amurka

A ranar 6 ga watan Oktoba, mamban hukumar siyasa na kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis kana daraktan ofishin hukumar harkokin kasashen wajen kasar Sin, Yang Jiechi, ya gana da Jake Sullivan, mataimakin sakataren al’amurran tsaro na shugaban kasar Amurka, a birnin Zurich, na kasar Switzerland. Bangarorin biyu sun amince da daukar matakan yin aiki tare domin ingiza dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka domin kyautata alakar kasashen da samar da ci gaba mai dorewa.

Kusan wata guda da ya gabata, a yayin tattaunawa ta wayar tarho da shugaba Biden na Amurka, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, batun dangantakar Sin da Amurka batu ne da ya zama wajibi a kyautata shi. A wancan lokacin, shugaba Biden shi ma ya fidda wani sakon neman bukatar tattaunawa da kuma yin hadin gwiwa.

A shekarun baya bayan nan, dangantaka tsakanin Sin da Amurka ta yi matukar tabarbarewa. Dalilin haka shi ne, saboda Amurka tana mummunar rashin fahimta game da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Don haka, karfafa tuntubar juna tsakanin sassan biyu, muhimmin mataki ne da zai kyautata hulda dake tsakanin Sin da Amurka. (Ahmad)