logo

HAUSA

MDD ya yi tir da barazanar wasu matasa kan jami’an ta dake yankin Pibor na Sudan ta Kudu

2021-10-06 16:02:38 CRI

Babban jami’in tsare tsaren ayyukan jin kai na MDD a Sudan ta kudu Matthew Hollingworth, ya yi Allah wadai da barazanar wasu matasa ‘yan zaman kashe wando, kan jami’an majalissar dake aiki a yankin Pibor mai fama da tashe tashen hankula.

Mr. Hollingworth, ya yi tir da matakin ne a ranar Litinin, bayan da matasan ‘yan zauna gari banza suka bukaci a kalla jami’an jin kai 30 dake aiki a yankinsu da su fice cikin sa’o’i 72.

Jami’in wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Talata a birnin Juba, fadar mulkin kasar, ya ce matasan sun zargi jami’an jin kan da aka tura yankin su daga wasu sassan kasar, da mallake wasu guraben ayyuka da ya kamata a baiwa ‘yan asalin yankin. (Saminu)