logo

HAUSA

Bayan Kin Gaskiya Sai Bata

2021-10-06 19:57:35 CRI

Bayan Kin Gaskiya Sai Bata_fororder_211006-sharhi-Ibrahim-hoto

Shaidu na kara bayyana game da asalin kwayar cutar COVID-19, abin da ke kara nunawa masu neman siyasantar da barin cewa, wannan batu ne da ya shafi kimiya. Sai dai abin takaici shi ne, duk da irin wadannan kwararan shaidu na sakamakon bincike masana kimiya daga sassa daban-daban na duniya, har yanzu wasu kasashen yammacin duniya da ‘yan korensu, na ci gaba da nunawa wasu yatsa game da asalin wannan cuta. Wanda ya yi nisa aka ce baya jin kira.

Amma duk kokarin da suke yi na neman mayar da hannun agogo baya a aikin binciken gano asalin kwayar cutar ta hanyar kimiya bisa shaidu na gaskiya da nuna gaskiya da adalci, da ma neman bata sunan wasu kasashe, don biyan muradunsu na siyasa, ba zai taba yin nasara ba.

Wani sabon sakamakon bincike na baya-bayan nan ada aka wallafa a shafin Intanet game da annobar ta COVID-19, ya gabatar da shaidu masu karfi dake goyon bayan hasashen da aka yi a kan COVID-19, tare da sakamakon da ke da wuyar daidaitawa gami da hasashen da wasu ke yi wai, kwayar cutar ta bulla ne daga dakin bincike.

Binciken farko na kwayoyin cuta da aka gano daga mutanen da suka kamu da cutar a farkon cutar SARS-CoV-2, ya nuna cewa, kwayar cutar da ke haifar da COVID-19, na iya yaduwa daga dabbobi zuwa ga mutane sau da yawa.

Sabon bincike, wanda aka wallafa a dandalin tattaunawa na virological.org, ya dogara ne a kan cikakken binciken jerin kwayoyin halittar tsare-tsare guda biyu na farko, da aka sani da A da B, wadanda ke da muhimman bambance bambancen kwayoyin cuta, wadanda kuma aka samo daga samfuran jinin mutanen da suka kamu da cutar a karshen 2019 da farkon shekarar 2020.

Ga mai hankali da wanda ya fahimci bincike na kimiya ya san cewa, tunanin da wasu ke yi na cewa, wai kwayar cutar ta bulla ne daga dakin gwaji, ba abu ne mai miyuwa ba, kamar yadda masana suka sha bayyanawa.

An ruwaito masanin ilimin kwayoyin cututtuka a jami’ar Tulane da ke New Orleans, a Louisiana ta kasar Amurka Robert Garry yana cewa, wannan babban bincike ne mai mahimmanci,sannan za a iya nuna cewa A da B layin jinsi ne guda biyu kuma akwai kwarara guda biyu, sannan yana kawar da ra'ayin cewa, cutar ta bulla ne daga dakin gwaje-gwaje. Kukan kurya ce dai jawabi…(Ibrahim Yaya)