logo

HAUSA

Wakilin Sin: Tsarin sarrafa makamai da kwance damara na bangarori daban daban yana kan hanya

2021-10-06 19:55:03 CRI

Jiya ne, babban zauren MDD na 76 da kwamitin kwance damarar makamai da tsaron kasa da kasa suka gudanar da muhawara. Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, a halin yanzu, tsarin sarrafa makamai da kwance damarar bangarori daban daban yana kan hanya, kuma kasashen duniya na fuskantar muhimmin zabi dangane da inda aka dosa.

A cikin jawabin nasa, Geng Shuang ya soki matakan da Amurka ta dauka wajen inganta makaman nukiliyarta, da ci gaba da gina tsarin yaki da makamai masu linzami na duniya, da bunkasa hadin gwiwar jiragen ruwa masu amfani da makamashin nukiliya tare da Birtaniya da Australia. (Ibrahim)