logo

HAUSA

Sin da Najeriya suna murnar bikin ranar 1 ga watan Oktoba tare

2021-10-05 11:50:09 CRI

Sin da Najeriya suna murnar bikin ranar 1 ga watan Oktoba tare_fororder_321

Ranar 1 ga watan Oktoba, rana ce ta cika shekaru 61 da tarayyar Najeriya ta samu ‘yanci daga turawan mulkin mallaka, kana rana ce ta cika shekaru 72 da kafuwar Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin. A daidai wannan lokaci, Murtala Zhang ya zanta da wasu mutanen kasashen biyu, don jin ra’ayinsu kan dangantakar dake tsakanin Sin da Najeriya.

Tarayyar Najeriya da Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin sun dade suna kokarin raya huldodinsu a fannoni daban-daban, ciki har da inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma, da kasuwanci da aikin gona da harkokin sadarwa da na ilimi da al’adu da sauransu. A halin yanzu akwai daliban Najeriya da dama wadanda suke karo ilimi a jami’o’in kasar Sin daban-daban, kana kuma akwai daliban kasar Sin da suke kokarin koyon yaren Hausa, abun da ya shaida dadadden zumunci da fahimtar juna tsakanin al’ummomin kasashen biyu.

Sin da Najeriya suna murnar bikin ranar 1 ga watan Oktoba tare_fororder_微信图片_20211005114238

Malam Nuraddeen Ibrahim Adam, ya fara koyar da harshen Hausa a jami’ar koyon harsunan waje ta Tianjin dake kasar Sin daga watan Satumbar shekara ta 2017, zuwa watan Yulin shekara ta 2021, wato shekaru hudu ke nan. Ya bayyana ra’ayinsa kan muhimmancin musanyar al’adu tsakanin Najeriya da Sin.

Ma Chang, ko kuma Safiya a yaren Hausa, daliba ce ta malam Nuraddeen a jami’ar koyon harsunan waje ta Tianjin, kana sabuwar ma’aikaciya ce wadda za ta fara aiki a sashin Hausa na rediyon kasar Sin wato CRI a shekara mai kamawa, ita ma ta bayyana burinta na kara bada gudummawa wajen karfafa hadin-gwiwa da zumunta tsakanin Sin da Najeriya.

Sin da Najeriya suna murnar bikin ranar 1 ga watan Oktoba tare_fororder_微信图片_20211005114245

Har wa yau, akwai mutanen kasar Sin da dama wadanda a yanzu haka suke aiki a birane da garuruwa da dama a Najeriya, musamman Abuja, Lagos, Kano da sauransu. Mista Kyle Cheng na daya daga cikinsu, wanda ke aiki a wani shahararren kamfanin sadarwar zamani na kasar Sin dake Abuja. Kyle, wanda ya shafe shekaru hudu da rabi yana aiki a Najeriya, ya ce abun da ya fi burge shi, shi ne yadda shi da abokansa ‘yan Najeriya suka nuna wa juna kulawa da kauna a yayin da ake kokarin dakile yaduwar cutar COVID-19 cikin hadin-gwiwa. Mista Kyle ya ce:

“Kusan kowace rana mu kan bugawa juna waya don gaisawa. Wasu lokuta ma mu kan baiwa juna kyautar wasu kayan yaki da cutar COVID-19. Nunawa juna kulawa ya kwantar da hankalinmu sosai musamman a lokacin kulle, kuma rayuwarmu ta koma hanya kamar yadda ya kamata. Mu kan gayawa junanmu cewa, ya kamata mu sanya abun rufe baki da hanci, gami da daukar abun fesawa na kashe kwayoyin cuta. Duk wadannan abubuwa sun sa na ji dadin rayuwa a Najeriya, duk da cewa ina nesa da kasata wato kasar Sin.”

Sin da Najeriya suna murnar bikin ranar 1 ga watan Oktoba tare_fororder_rBABCmBYbqCADLfpAAAAAAAAAAA380_650x432

A nasa bangaren, Sheriff Ghali Ibrahim, darektan cibiyar horas da ‘yan majalisu na jami’ar Abuja, wanda kuma shi ne shahararren masanin harkokin kasar Sin a tarayyar Najeriya, ya bayyana ra’ayinsa kan dangantakar abokantaka dake tsakanin Sin da Najeriya, musamman shawarar “ziri daya da hanya daya”. (Murtala Zhang)