An samu malalar danyen mai a gabar teku ta jihar California
2021-10-05 21:18:50 CRI
Kwanan nan aka samu malalar danyen mai a gabar teku da ke gundumar Orange ta kudancin jihar California ta kasar Amurka, lamarin da ya haifar da babbar barazana ga muhallin wurin. Yanzu gwamnatin wurin ta fara tsabtace sassan da suka gurbata.(Lubabatu)