logo

HAUSA

Kashin farko na gudummawar alluran rigakafin COVID-19 da gwamnatin kasar Sin ta baiwa Mali ya isa Bamako

2021-10-05 20:11:21 CRI

Kashin farko na gudummawar alluran rigakafin COVID-19 da gwamnatin kasar Sin ta baiwa Mali ya isa Bamako_fororder_mali

A cewar shafin yanar gizon ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Mali, a yammacin jiya Litinin 4 ga watan Oktoba, agogon wurin ne, rukunin farko na alluran rigakafin COVID-19 da gwamnatin kasar Sin ta baiwa kasar Mali karkashin shirin nan na COVAX, ya isa Bamako, babban birnin kasar ta Mali.

Ministan kiwon Lafiya da ci gaban al'umma na Mali Diminatou Sangare, ya nuna godiyarsa ga kasar Sin tare da bayyana cewa, wannan gudummawar za ta taka muhimmiyar rawa sosai wajen kandagarki da shawo kan cutar a Mali. Sangare ya ce, za a aika allurar rigakafin da kasar Sin ta bayar cikin sauri zuwa dukkan sassan kasar, kuma gwamnati za ta fara aikin rigakafin cikin gaggawa.(Ibrahim)