Demokradiyya Ta Hakika Ita Ce Mai Dacewa Da Yanayin Kasa Da Kare Muradun Al’ummarta
2021-10-05 19:38:35 CRI
Duk da cewa makomar bil adama na hade da juna, yanayin yankunan duniya, ko nahiyoyi ko shiyyoyi da uwa uba kasashe, ya bambamta. Haka zalika dabi’u da al’adu da addini. Kasancewar wannan bambanci ya sa dole al’ummomin duniya su girmama juna muddun ana son zaman lafiya.
Tsarin da ya dace da wata kasa, ba lallai ne ya samu karbuwa ko mazauni a kasar dake makwabtaka da ita ba, bare kuma wata kasa dake wata nahiya ta daban.
Yayin taron majalisar kare hakkin dan adam karo na 48 a birnin Geneva, jakadan kasar Sin Chen Xu, ya jaddada a jiya cewa, bai kamata wasu tsirarrun kasashe su tsara yadda ainihin demokradiyya zata kasance ba.
Hausawa kan ce, mai daki shi ya san inda ke masa yoyo. Ba zai taba yuwuwa a ce wata kasa daga can waje ce za ta tsara yadda wata za ta jagoranci jama’arta ba. Abu mafi muhimmanci ga tsarin shugabanci shi ne, kare ‘yancin kasa da muradun da tsaro da walwalar jama’arta.
Misali, tafarkin da kasar Sin ta dauka na neman ci gaba, ya sha bambam da wadanda kasashen yamma suka dauka, kuma dukkan shaidu sun nuna yadda cikin kankanin lokaci, kasa da lokacin da kasashen na yamma suka dauka wajen samun ci gaba, kasar Sin ta kai matsayin kasa mafi karfin tattalin arziki na biyu a duniya, duk da cewa kasa ce mai tasowa. Haka zalika al’ummarta da yawansu ya kai biliyan 1.4, su na cikin walwala da kwanciyar hankali, kuma ba sa korafi dangane da tafarki da tsaruka da dabarun da gwamnatinsu ta dauka. Lamarin dake nuna cewa, sun aminta kuma suna goyon bayanta dari bisa dari. Don haka bai kamata a rika fakewa da tsarin demokradiyya wajen yi wa Sin shisshigi ko bata mata suna ko yunkurin dakile ci gabanta ba. Kasar Sin ta sha nanata cewa, duk irin ci gaban da za ta samu, ba za ta taba mamaya ko babakere ko kakaba tsarukanta kan wasu ba, duk kuwa da cewa a kullum kasashe masu tasowa na nuna sha’awarsu ga irin tafarkin da ta zabarwa kanta. Babu makawa, da dukkan kasashe za su nazarci tsarin demokradiyya da ya yi daidai da yanayin da suke ciki, da sun samu ci gaba da kwanciyar hankali kamar Sin.
Ya kamata kasashen masu daukar Sin a matsayin abokiyar hamayya, su mayar da hankali kan matsalolin da suke fuskanta, su yi kokarin raya kansu da al’ummarsu maimakon bata lokaci wajen yi mata makarkashiya. Zaman tare cikin lumana shi ne, girmama bambance bambancen dake akwai da kuma cikakken ikon da kowacce kasa ke da shi. (Fa’iza Mustapha)