logo

HAUSA

Kasar Sin ta gargadi Amurka ta daina nuna wariya da girman kai

2021-10-05 15:37:58 CRI

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya jaddada cewa, kasar Sin na matukar adawa da amfani da batutuwan hakkin dan Adam wajen takalarta.

Zhang Jun ya bayyana haka ne da yake jawabi yayin muhawarar da kwamiti na 3 na babban zauren MDD na 76, ya ci gaba da yi a jiya Litinin.

Jawabin nasa, martani ne ga tsoma baki da furucin da Amurka ke yi kan batutuwan da suka shafi yankunan Xinjiang da Hong Kong da Tibet na kasar Sin.

A cewarsa, ya kamata Amurka ta daina tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin, kana ta yi watsi da girman kai da wariyar da take nunawa nan take, domin kaucewa ci gaba da bin hanyar da ba ta dace ba da kara tafka kura kurai. (Fa’iza Mustapha)