logo

HAUSA

Sabbin shaidu sun nuna COVID-19 ta bulla daga dabbobi zuwa ga mutane sau da dama

2021-10-04 16:25:54 CRI

Sabbin shaidu sun nuna COVID-19 ta bulla daga dabbobi zuwa ga mutane sau da dama_fororder_病毒-4

Wani sabon bincike da aka wallafa a shafin yanar gizo a kwanan nan, ya gabatar da shaidu masu karfi dake goyon bayan hasashen da aka yi a kan COVID-19, tare da sakamakon da ke da wuyar daidaitawa gami da hasashen da wasu ke yi wai, kwayar cutar ta bulla ne daga dakin bincike.

A cewar binciken farko na kwayoyin cuta da aka gano daga mutanen da suka kamu da cutar a farkon cutar SARS-CoV-2, kwayar cutar da ke haifar da COVID-19, na iya yaduwa daga dabbobi zuwa ga mutane sau da yawa.

Sabon bincike, wanda aka wallafa a dandalin tattaunawa na virological.org, ya dogara ne a kan cikakken binciken jerin kwayoyin halittar tsararraki biyu na farko, da aka sani da A da B, wadanda ke da muhimman bambance bambancen kwayoyin cuta, wadanda kuma aka samo daga samfuran jinin mutanen da suka kamu da cutar a karshen 2019 da farkon shekarar 2020.

Wannan babban bincike ne mai mahimmanci. Idan za ku iya nuna cewa A da B layin jinsi ne guda biyu kuma akwai kwarara guda biyu, komai yana kawar da ra'ayin cewa, ya bulla ne daga dakin gwaje-gwaje, kamar yadda labarin halitta ya ruwaito Robert Garry, masanin ilimin kwayoyin cututtuka a jami'ar Tulane da ke New Orleans, dake Louisiana, ya bayyana.(Ibrahim)