logo

HAUSA

Dan kasuwa a Zambia na samarwa iyalai marasa wadata takalma masu rahusa

2021-10-04 16:17:27 CRI

Samun takalma kan farashi mai rahusa, kalubale ne ga iyalai masu karancin kudin shiga, har ma da daidaikun mutane a kasar Zambia.

Sai dai ga mutane da dama dake gundumar Kafue, wadda ke kudancin Lusaka, babban birnin Zambia, an riga an shawo kan wannan kalubale kimanin shekaru 20 da suka gabata, bayan kafa kamfanin Tusole, dake samar da takalman fata da ake kira da MOSNA shoes.

Mamallakin kamfanin Moses Nachibanga mai shekaru 61, ya ce ya shiga harkar samar da takalma ne bayan ya fuskanci kalubale wajen samun takalma masu rahusa ga ‘ya’yansa. Lamarin da ya sa ya ajiye aikinsa, ya shiga sana’ar samar da takalma.

“Ba ni da isasshen kudin sayen takalman makaranta ga ‘ya’yana, don haka na sa wani mai gyaran takalma ya yi musu. Duk da irin kayayyakin da ya yi amfani da su, na ga kwarewa a tare da shi, don haka na yanke shawarar hada gwiwa da shi. Na yi amfani da kudin ritayata wajen sayo kayayyakin aiki masu kyau.”

Ya kara da cewa, harkar da aka fara da zummar samar da takalma masu rahusa ga iyalai marasa wadata a gundumar Kafue, ya habaka zuwa harkar kasuwanci dake jan hankalin mutane daga dukkan bangarori na rayuwa. (Fa’iza Mustapha)