logo

HAUSA

An zabi Fumio Kishida a matsayin firaministan Japan

2021-10-04 15:41:09 CRI

An zabi Fumio Kishida a matsayin firaministan Japan_fororder_firayiminstan Japan

An zabi Fumio Kishida, shugaban jam’iyyar LDP mai mulkin kasar Japan a matsayin sabon firaministan kasar da zai maye gurbin Yoshihide Suga.

Yayin da kawancen jam’iyyu dake karkashin jam’iyyar LDP ke da rinjaye a dukkan majalisun kasar, Fumio Kishida mai shekaru 64, ya samu kuri’u mafi rinjaye a majalisar wakilai da ta dattijai.

Bayan sanar da ministocinsa a yau da rana, za a rantsar da Kishida yayin wani biki da za a yi a fadar Imperial, inda daga bisani zai kira taron manema labarai da yammacin yau din.

Kalubale na farko da kishida zai fuskanta shi ne babban zaben kasar. Yana shirin gudanar da zaben ne a ranar 31 ga watan Oktoba, yayin da ‘yan majalisar wakilai za su fara gangamin yakin neman zabe daga ranar 19 ga wata. (Fa’iza Mustapha)