logo

HAUSA

Yawan wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a nahiyar Afrika ya zarce miliyan 8.33

2021-10-04 15:45:28 CRI

Cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Afrika, ta ce adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a nahiyar ya kai 8,333,206, zuwa yammacin jiya Lahadi.

Cibiyar ta ce adadin wadanda cutar ta yi sanadin rayukansu a fadin nahiyar ya kai 212,055. Sai kuma wasu 7,671,969 da suka warke daga cutar.

A cewarta, kasashen Afrika ta kudu da Morocco da Tunisisa da Habasha na daga cikin kasashen da suka fi fama da cutar.

Ta kara da cewa, kudancin nahiyar ne cutar ta fi addaba, sai yankin arewacin nahiyar dake bi masa baya, sai kuma yankin gabashi, yayin da tsakiyar nahiyar ke da adadi mafi karanci na wadanda suka kamu da cutar a nahiyar. (Fa’iza Mustapha)