logo

HAUSA

Sojojin kiyaye zaman lafiya da Sin ta tura DRC a karo na 25 sun isa wurin aiki

2021-10-03 15:41:30 CRI

Sojojin kiyaye zaman lafiya da Sin ta tura DRC a karo na 25 sun isa wurin aiki_fororder_DRC

Sojojin wanzar da zaman lafiya 94 da kasar Sin ta turawa Jamhuriyar Demokudariyar Congo a karo na 25 a mataki na biyu, sun isa wurin aikinsu dake jihar Kivu ta kudu a jiya Asabar, lamarin da ya alamta cewa, daukacin jami’an tsaron da kasar Sin ta tura kasar a karo na 25, sun riga sun sauka a wurin aikinsu.

Adadin sojojin da kasar Sin ta turawa DRC a karo na 25 ya kai 218 wadanda suka hada injiniyoyi 175 da ma’aikatan kiwon lafiya 43, wasu sun isa wurin aiki a ranar 12, kana suka fara aiki a ranar 28 ga watan Satumban da ya gabata, inda suka maye gurbin takwarorinsu da kasar Sin ta tura a karo na 24.

Kasar Sin ta turawa Jamhuriyar Demokradiyyar Congo sojojin wanzar da zaman lafiya a karon farko ne a watan Afililin shekarar 2003, bisa gayyatar da MDD ta yi mata. Kawo yanzu, gaba daya adadin sojojin kasar Sin dake wanzar da zaman lafiya a DRC ya riga ya kai sama da 3000.(Jamila)