logo

HAUSA

Likitocin Sin suna kokarin ingiza ci gaban kiwon lafiya a Zimbabwe

2021-10-03 15:42:44 CRI

Likitocin Sin suna kokarin ingiza ci gaban kiwon lafiya a Zimbabwe_fororder_likita.JPG

Duk da cewa annobar cutar numfashi ta COVID-19 tana ci gaba da yaduwa a fadin duniya, wasu likitocin da kasar Sin ta turawa kasashen waje domin ba da tallafi suna ci gaba da gudanar da aikinsu na ceton rayukan jama’a a sassa daban daban na fadin duniya.

Jiang Jiarui, wanda ya taba aiki a asibitin cutar kansa na lardin Hunan na kasar Sin, daya ne daga cikin tawagar ma’aikatan kiwon lafiya da kasar Sin ta turawa Zimbabwe, inda yanzu yake aiki a asibitin Parirenyatwa dake kasar. Ya kuma shaida mana cewa, “Ana kiran likitocin da aka turawa ketare domin ba da tallafi, da sunan jami’an diplomasiyya masu sa kayan likita, gaskiya ne muna gudanar da aiki a madadin kasarmu.”

Yanzu haka suna fuskantar matsaloli daban daban sakamakon yaduwar annobar COVID-19, amma Jiang Jiarui ya bayyana cewa, zai ci gaba da aiki a kasar ta Zimbabwe, ta yadda zai kammala aikin ba da tallafin kiwon lafiya a ketare, da kasarsa ta ba shi.(Jamila)