logo

HAUSA

Rahoton The Lancet: Yawan mutanen da suka mutu sakamakon cin zarafin yan sandan Amurka ya zarce alkaluman hukumomi

2021-10-02 16:35:40 CRI

Wani rahoton bincike na baya bayan nan da mujallar kiwon lafiya ta kasa da kasa wato "The Lancet" ya nuna cewa, a cikin shekaru 40, adadin mutanen da suka mutu a sanadiyyar cin zarafi da jami’an ‘yan sandan kasar Amurka suka yi musu, an kwashe sama da kaso hamsin bisa dari na adadin idan an kwatanta da hakikanin alkaluman.

An kwatanta alkaluman da hukumomin Amurka suka bayyana da wadanda ma’ajiyar adana bayanai na bangarori uku na al’umma suka adana, game da alkaluman mutanen da jami’an tsaron suka ci zarafinsu ta hanyar kisa, masu binciken sun gano cewa tun a shekarun 1980, an samu adadin mutanen da suka mutu sama da 17,000 a sakamakon gallazawar da ‘yan sandan Amurka suka yi musu, ko dai ba a tantance adadin yadda ya kamata ba ko kuma ba a adana cikin ma’ajiyar bayanan gwamnati ba. Kusan kashi 60% na Amurkawa ‘yan asalin Afrika da suka mutu sakamakon muzgunawar ‘yan sandan, ko dai ba a bayyana su ba ko kuma an yi kuskure wajen kididdige su.

Marubucin wannan nazari ya bayyana cewa, bayanan bogi ko kuma rashin kididdige wadannan mace-macen da aka samu zai kara boye girman mummunar matsalar nuna wariyar da hukumomin tabbatar da tsaron Amurka ke aikatawa.(Ahmad)