logo

HAUSA

Shugaban Nijeriya ya yi kira da a gaggauta rabon rigakafin COVID-19 cikin adalci

2021-10-02 15:17:50 CRI

Shugaban Nijeriya ya yi kira da a gaggauta rabon rigakafin COVID-19 cikin adalci_fororder_Buhari

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya yi kira ga kasashen duniya su gaggauta rabon rigakafin COVID-19 cikin adalci, a matsayin wata hanya ta taimakon juna wajen yaki da annobar.

Da yake jawabi domin ranar samun ‘yancin kai ta kasar a jiya, Muhammadu Buhari ya ce zai yi amfani da damar wajen tunatarwa duniya cewa, yanayin da ake ciki na rabon rigakafin bai dace ba sam. Ya ce ba zai yiwu a ce wasu kasashe tsiraru ne suka tanadarwa kansu rigakafin ba, yayin da sauran kasashe ke fuskantar karancinsa.

Ya ce dole ne a dauki mataki yanzu a gaggauta rabon rigakafin. Yana mai cewa, ya riga ya aike da sako ga kasashen duniya a makon da ya gabata a birnin New York, yayin muhawarar babban zauren MDD.

Ya kara da cewa, kawo yanzu, an yi wa ‘yan Nijeriya amfani da allurai miliyan 5 bisa kokarin hukumar kula da lafiya a matakin farko ta kasar. Yana mai cewa, a shirye kasar take ta ci gaba da lalubo hanyoyin sayen rigakafin ta hannun shirin COVAX ko kuma asusun sayen rigakafi na Afrika. (Fa’iza Mustapha)