logo

HAUSA

Za a rantsar da shugaban juyin mulkin sojin Guinea a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya a 1 ga Oktoba

2021-10-01 16:31:57 CRI

An rantsar da shugaban juyin mulkin sojin Guinea a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya a 1 ga Oktoba_fororder_1

Kafar yada labarai ta Guinea News Network, ta bayyana cewa, sojojin da suka jagoranci juyin mulki a kasar Guinea sun sanar cikin wani jawabi ta gidan talabijin din kasar da aka watsa da yammacin ranar 29 ga watan Satumba agogon kasar cewa, madugun juyin mulkin sojojin kasar  Guinea, Mamadi Doumbouya zai kasance a babban birnin kasar Conakry a ranar 1 ga watan Oktoba. Inda za a rantsar da shi a fadar shugaban kasa a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwaryar kasar.

A bisa ga yarjejeniyar mika mulki ta sojojin da suka jagoranci juyin mulkin na ranar 27 ga watan Satumba sun sanar cewa, Mamadi Dumbuya shi ne zai kasance shugaban kasar na rikon kwarya, kuma a matsayinsa na shugaban kasa na rikon kwarya, sannan shi ne zai jagoranci kafa gwamnatin rikon kwaryar kasar wadda firaminista zai shugabance tare da mambobin kwamitin rikon kwarya na kasa CNT kimanin 81.(Ahmad)