logo

HAUSA

An rantsar da madugun juyin mulkin sojin Guinea a matsayin shugaban kasa na rikon kwarya

2021-10-01 21:16:55 CRI

A yau Juma’a 1 ga watan Oktoba, aka rantsar da shugaban juyin mulkin sojojin kasar Guinea, Mamadi Doumbouya, a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya a babban birnin kasar Conakry. A bisa ga dokar yarjejeniyar mika mulki na kasar wanda kwamitin hadin kai da ci gaban kasar Guinea ya amince da shi a ranar 27 ga watan Satumba,  Doumbouya ne zai kafa gwamnatin rikon kwarya wadda firaminista zai shugabance tare da mambobin kwamiti na gwamnatin rikon kwaryar wanda zai kumshi mambobi kimanin 81.(Ahmad)