logo

HAUSA

Masani: Ya dace Zambia ta yi amfani da CAETE don janyo hankalin masu zuba jari

2021-09-30 10:25:47 CRI

Masani: Ya dace Zambia ta yi amfani da CAETE don janyo hankalin masu zuba jari_fororder_210930-Ahmad 1

Wani masanin dangantakar kasa da kasa ya ce, ya kamata kasar Zambia da sauran kasashen Afrika su yi kyakkyawan amfani da bikin baje kolin raya tattalin arziki da bunkasa cinikayya na Sin da Afrika wato CAETE, wanda kasar Sin ta shirya domin su tallata hajojinsu ga kamfanonin masu sha’awar zuba jari daga kasar Sin.

Aaron Siwale, malami kuma manazarci a sashen kimiyyar siyasa da harkokin mulki na jami’ar kasar Zambia (UNZA), ya ce bai kamata a yi sakaci da wadannan damammaki masu tarin yawa ba sakamakon yadda kamfanoni masu yawa suka halarci bikin baje kolin.

A tsokacin da ya yi a wajen bikin CAETE karo na biyu wanda aka bude a ranar Lahadin da ta gabata, wanda ya janyo hankalin kamfanoni kusan 900 daga kasashen Afrika kusan 40 da kasar Sin a Changsha, babban birnin lardin Hunan, masanin ya ce, bikin ya samar da muhimmiyar dama ga kasashen Afrika ta yadda za su tallata fannonin zuba jarinsu.

A zantawarsa da manema labarai masanin ya ce, idan ka duba Zambia, akwai albarkatun kasa masu yawa, kuma wannan kadai wata muhimmiyar dama ce ta janyo hankalin masu zuba jari daga abokan hulda. Kuma ya dace a rungumi irin wannan biki da hannu biyu-biyu.

Kwararren ya ce kamata ya yi Afrika ta yi amfani da kyakkyawar alakar dake tsakaninta da kasar Sin wajen cin moriyar kwarewar da kasar ke da shi a fannin fasahohi. Ya kara da cewa, duk da dunbum albarkatun da ake da su, Afrika tana fama da matsalar karancin fasaha da manyan injunan sarrafa albarkatu don samar da kayayyakin da ake bukata. (Ahmad Fagam)