logo

HAUSA

Sin Ta Gabatarwa Duniya Hanyar Yaki Da Cutar COVID-19 Mai Cike Da Nasarori

2021-09-30 17:26:37 CRI

Sin Ta Gabatarwa Duniya Hanyar Yaki Da Cutar COVID-19 Mai Cike Da Nasarori_fororder_src=http___dingyue.ws.126.net_2020_0312_14d9296fj00q71hbj000md200p000ang00p000an&refer=http___dingyue.ws.126

Daga Saminu Alhassan

Sama da shekara guda, cutar COVID-19 na ci gaba da zame wa duniya kadangaren bakin tulu, kuma wani irin kalubale mai wuyar sha’ani ga masu tsara manufofi, ta yadda kasashe da yankunan duniya daban daban, ke ta hankoron daidaita manufar kiwon lafiyar al’umma, da batun rage radidin da sashen raya tattalin arziki ke fuskanta.

Da farko farkon bazuwar wannan annoba, kasar Sin ta fuskanci yaduwarta kamar sauran kasashen duniya, amma matakai da aka dauka cikin gaggawa, da rungumar kimiyya a matsayin madogara, sun baiwa mahukuntan kasar damar shawo kan annobar yadda ya kamata. Kaza lika hakan ya ingiza ci gaban tattalin arzikin kasar, fiye da ma kafin bullar annobar. Hakan ne ya sa da yawa daga masu fashin baki ke kallon matakan da Sin ke aiwatarwa, a matsayin zakaran gwajin dafi a fannin yaki da wannan annoba.

Ko shakka ba bu, jam’iyyar Kwaminis mai mulkin kasar Sin, da gwamnati da daukacin al’ummar Sinawa, sun yi namijin kokari wajen daidaita matakan shawo kan cutar COVID-19, da manufofin bude harkokin tattalin arziki. An aiwatar da matakan kare lafiyar al’umma, da maida ran bil adama gaban komai, ta yadda hakan ya haifar da karin damammaki ga kasar.

A bayyane take cewa, duk da tarin kalubale da barkewar annobar COVID-19 ya haifar ga kasar Sin, ta fuskar bukatar aiwatar da matakai masu tsauri na shawo kan ta, da tsara manufofin dakile sake bullar ta, a hannu guda kuma, annobar ta wajabtawa kasar Sin hawa wata turba mai muhimmanci, ta tsara manufofin tunkarar makamantan irin wannan annoba a nan gaba. Har ila yau, kasar Sin ta cimma nasarar sake bude sassan tattalin arziki, da harkokin zamantakewar al’umma yadda ya kamata.

Bugu da kari, kasar Sin ta samar da gagarumar gudummawa ga sauran sassan duniya, musamman kasashe masu tasowa, ta yadda za su tunkari kalubalen yaduwar cutar, kama daga ba su tallafin kayan yaki da cutar, zuwa raba tallafin rigakafi cikin gaggawa.

Lura da wadannan matakai, da manufofi, tare da tsare tsare da Sin ke ci gaba da aiwatarwa a fannin yaki da annobar COVID-19, a iya cewa Sin ta ciri tuta, ta kuma gabatarwa duniya wata sahihiyar hanya mafi inganci ta yaki da cutar COVID-19 wadda ke cike da nasarori. (Saminu Alhassan)