logo

HAUSA

Ofishin jakadancin kasar Sin dake Nijer ya shirya bikin murnar cika shekaru 72 kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin ta yanar gizo

2021-09-30 10:41:10 CRI

Ofishin jakadancin kasar Sin dake Nijer ya shirya bikin murnar cika shekaru 72 kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin ta yanar gizo_fororder_210930-Ahmad 2

A ranar 28 ga watan Satumba, ofishin jakadancin kasar Sin dake jamhuriyar Nijer ya gabatar da bikin murnar cika shekaru 72 da kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin ta kafar intanet. Jiang Feng, jakadan kasar Sin a Nijer, ya gabatar da jawabi ta kafar intanet, yayin da Hassoumi Massoudou, ministan harkokin wajen jamhuriyar Nijer, ya gabatar da jawabinsa ta kafar bidiyo a madadin gwamnatin Nijer.

Jakada Jiang ya ce, shekarar 2021 wata muhimmiyar shekara ce ga kasar Sin. A wannan shekarar ne aka yi bikin murnar cika shekaru 100 da kafuwar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ta kasance mafarin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14. Jakada Jiang ya bayyana cewa, a koda yaushe kasar Sin za ta kasance a matsayin mamba a rukunin kasashe masu tasowa. Wannan shi ne tsarin siyasar da Sin ta zaba kuma za ta ci gaba da bayar da gagarumar gudummawa wajen daga matsayin ci gaban kasashe masu tasowa. Jakada Jiang ya nanata cewa, huldar dake tsakanin Sin da Nijer ta samar da muhimman sakamako. Kasar Sin tana burin hada shirin raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 14 da zagaye na uku na shirin farfado da jamhuriyar Nijer domin bunkasa dukkan fannonin yarjejeniyar hadin gwiwar kawance da Sin da Nijer.

Ofishin jakadancin kasar Sin dake Nijer ya shirya bikin murnar cika shekaru 72 kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin ta yanar gizo_fororder_210930-Ahmad 2-hoto2

A madadin gwamnatin Nijer, ministan harkokin wajen kasar Nijer Hassoumi Massoudou, ya taya murnar cika shekaru 72 da kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, ya yaba da kyakkyawar huldar dake tsakanin Nijer da Sin tare da burin ci gaba da karfafa huldar dake tsakanin kasashen biyu, kana ya yabawa kasar Sin bisa gudunmawa masu tarin yawa da take baiwa Nijer don bunkasa cigaban tattalin arziki da zaman rayuwar al’ummar kasar. Ya bayyana cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Nijer da Sin tamkar abin koyi ne ga tsarin hadin gwiwar kasashe masu tasowa. A koda yaushe kasashen biyu suna girmama juna kana suna cin moriyar kyakkyawar huldar ’yan uwantaka dake tsakaninsu. (Ahmad)