logo

HAUSA

Kamata Ya Yi A Kalli Hakikanin Halin Da Sin Ke Ciki

2021-09-30 15:32:36 CRI

Kamata Ya Yi A Kalli Hakikanin Halin Da Sin Ke Ciki_fororder_00301790891_67e4bb05

Daga Amina Xu

Mene ne hakikanin halin da ake ciki a kasar Sin? Ya kamata ka zo ka ganewa idonka, idan ba ka da dama, zan fada maka wani labari dangane da wasu ‘yan Najeriya da suka kawo ziyara a nan kasar Sin.

Na yi aiki a Najeriya daga shekarar 2016 zuwa 2018. A tsawon wannan lokaci, na rufawa wata tawagar shugabannin kafofin yada labarai na Najeriya baya a ziyarar da suka kawo kasar Sin. Madam Olufunke Adeyinka Egbemode, tsohuwar shugabar kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya ita ce shugabar tawagar. Kafin ta kawo ziyara a nan kasar Sin, ta nuna cewa, idan Najeriya ba ta yi kokari ba, Sin za sha gabatanta. A zamanin da ita ma Sin ta yi fama da talauci da koma baya, inda zaman rayuwar jama’a babu tabbaci balle a ce a tabbatar da hakkin Bil Adama ko demokuradiyya. To amma yanzu wane irin hali Sin take ciki?

Madam Olufunke Adeyinka Egbemode ta jagoranci tawagar wasu shahararrun wakilai na jaridar “Newtelegraph” da FRCN da dai sauransu, inda suka ziyarci birane Beijing da Tianjin da sauransu, suka kuma ganewa idanunsu yadda Sin ta samu bunkasuwa a fannin tattalin arziki da al’adu da kimiyya da fasaha da sauransu. Kafin Madam Olufunke ta koma gida Najeriya, ta ce, Beijing ya fi New York kyau, saboda ba ma kawai Beijing na da manyan ababen more rayuwa masu inganci ba, har ma ana iya fita yawo da dare ba tare da wata matsala ba, Sin ya fi New York tsaro. Bayan dawowarta Najeriya, wasu manyan jaridu da shafukan yanar gizo da na shafukan sada zumunta, sun wallafa bayanai uku da ta rubuta mai suna “Wadanne abubuwa kafofin yada labarai na Najeriya za su koya daga kasar Sin?” da “Ya kamata Najeriya ta koyi dabarun saurin bunkasuwar Sin (1) da (2)”. Hausawa kan ce “gani ya kori ji”, saboda haka, matsayin da Madam Olufunke ta dauka ya canja matuka. Da haka, za a fahimci cewa, labaran da kafofin yada labarai na kasashen yamma suke watsawa a Afrika game da kasar Sin babu gaskiya, ya sabawa abin da Madam Olufunke da abokanta suka gani.

A ganina, abu mafi muhimmanci game da hakkin Bil Adama, shi ne tabbatar da hakkin zaman rayuwa mai kyau da bunkasuwa, idan babu isashen abinci ko tufafi ko gidaje, to yaya za a tabbatar da demokuradiyya da ‘yanci? Sin tana daukar matakai masu inganci wajen tabbatar da zamantakewar al’umma, a watan Fabrairu na bana, Sin ta sanar da tsame wasu mutane daga kangin talauci, matakin da ya nuna cewa, an tabbatar da zaman rayuwar Sinawa da dama, suna da tsaro da gidaje da isashen abinci da tufafi masu kyau, suna kuma jin dadin zaman rayuwarsu matuka, wannan shi ne mataki mafi kyau wajen tabbatar da hakkin Bil Adama. Ba shakka jama’a da suke jin dadin zama, za su goyi bayan gwamnatinsu, abin da zai ingiza bunkasuwar kasa gaba, hakan ya sa Sin ta samu ci gaba mai armashi a duniya. Ya kamata, a ba da tabbaci ga kare hakkin Bil Adama da demokuradiyya a matsayin wani mataki mai inganci don inganta zaman rayuwar jama’a, kuma hanya daya tilo da za a samu goyon bayan jama’a.

Duk mai nuna shakku game da yanayin hakkin Bil Adama ko demokuradiyya a kasar Sin, to ya kamata ya kawo ziyara a yankin Xinjiang ko Tibet da sauran wurare don ganewa idanunsu, idan kuma ba shi da dama, sai ya kalli hotunan bidiyoyin da al’ummar Sinawa suke wallafawa a yanar gizo, wadanda suka nuna ainihin zaman rayuwarsu a kasar Sin. Sai dai wasu kafofin yada labarai na kasashen yamma sun rufe shafukansu, watakila suna jin tsoro matuka don kada a fahimci hakikanin halin da ake ciki a kasar Sin. (Amina Xu)