logo

HAUSA

Wani rahoton bincike ya fayyace irin ci gaban da Sin ta samu a fannin kare hakkokin bil adama

2021-09-30 20:06:58 CRI

Wani rahoton bincike ya fayyace irin ci gaban da Sin ta samu a fannin kare hakkokin bil adama_fororder_hakki

Kungiyar masu bincike game da kare hakkin bil adama ta kasar Sin, da wasu cibiyoyin bincike na kasar, sun fitar da sakamakon wani nazari, inda rahoton da suka fitar ya nuna cewa, bisa sakamakon da kasar ta cimma, duniya ta shaida irin nasarori da Sin ta samu a fannin kare hakkin bil adama, karkashin shirin kasar na tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020.

Cikin rahoton da aka fitar a jiya Laraba, an bayyana irin kwazon JKS, da gwamnatin kasar, wajen gudanar da mulki don al’umma, ta yadda hakan ya haifar da manyan nasarori a fannin kare hakkin bil adama.

Kaza lika rahoton ya bayyana cewa, dalilin da ya sanya aka kai ga cimma wadannan nasarori shi ne, JKS na sanya al’umma gaban komai, ta kuma daidaita sassan ayyukan ci gaban kasa, da yanayin da kasar ta Sin ke ciki.

Bugu da kari, rahoton ya ce, a gabar da Sin ke shiga sabon mataki na samar da ci gaba, su ma ginshikan ta na kare hakkin bil adama na kara samun karfi. Kuma Sin na da karfin ikon ci gaba da cimma manyan nasarori a tarihin ta a wannan fanni.  (Saminu)