logo

HAUSA

Hukumar kula da makamashi ta duniya ta fitar da rahoton taswirar tsarin makamashi na kasar Sin maras gurbata muhalli

2021-09-29 21:04:52 CRI

Jiya ne hukumar kula da makamashi ta duniya, mai hedkwata a birnin Paris na Faransa, ta fitar da rahoto game da "Taswirar tsarin makamashin kasar Sin maras gurbata muhalli". Dangane da haka, Fatih Birol, darektan hukumar makamashi ta kasa da kasa, ya ce kasar Sin tana da karfin kammala sauyawa zuwa tsarin amfani da makamashi mai tsafta cikin sauri.(Ibrahim)